’Yan sanda sun harbi wanda ya saci akwatin zabe a Hadeja
’Yan sanda sun harbi wani mutun da ake zargin dan dabar siyasa ne inda ya samu munanan raunuka a daidai lokacin da ya yi kokarin sace akwatin zabe a mazabar Dubantu da ke Unguwar Yayari a garin Hadeja a Jihar Jigawa. Wannda ake zargin an ce ya sace akwatin ne a lokacin da ake kada […]
’Yan sanda sun harbi wani mutun da ake zargin dan dabar siyasa ne inda ya samu munanan raunuka a daidai lokacin da ya yi kokarin sace akwatin zabe a mazabar Dubantu da ke Unguwar Yayari a garin Hadeja a Jihar Jigawa.
Wannda ake zargin an ce ya sace akwatin ne a lokacin da ake kada kuri’a lamarin da ya sa aikin zaben ya tsaya cik, inda ’yan sandan da suke bakin aiki suka harbe shi a kokarin kwato akwatin zaben daga hannunsa, bayan sun yi masa duk wata barazana bai sauya ra’ayi ba.
’Yan sandan sun kuma garzaya da wanda ake zargin zuwa babban asibitin Hadeja domin yi masa jinya kafin su ci gaba da tuhumarsa kuma su gabatar da shi a gaban kotu kan karya dokokin zabe.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, DSP Audu Jinjiri, ya ce ba su samu labarin
aukuwar lamarin ba, lokacin da wakilinmu ya tuntube shi.