’Yan sanda sun kama ɓarayi 6, sun ƙwato motoci 5 a Kaduna 

Kakakin ya ce rundunar na ci gaba da yin bincike a kan waɗanda ake zargin.

’Yan sanda sun kama ɓarayi 6, sun ƙwato motoci 5 a Kaduna 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da ƙwato motoci biyar daga hannunsu.

Kakakin rundunar jihar, ASP Mansir Hassan ne, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.

Hassan ya ce, “Da misalin ƙarfe 3:10 a ranar Alhamis, tawagar ‘yan sanda daga Tudun Wada da ke Zariya, ta kama wani da ake zargi mai shekara 37 daga ƙaramar hukumar Faskari ta Jihar Katsina.”

Hassan ya kuma bayyana cewa a ranar Talata, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, sashen hana satar motoci ya gano wasu motoci guda biyu da aka bar su a gefen hanya.

Motocin guda biyun ƙirar Toyota Matrix (mai lamba DKA 321 TT) da Toyota Camry LE (mai lamba KGK 114 AA), a yankin Mogadishu da ke Kaduna.

Ya ƙara da cewa washegari a ranar Laraba, da misalin ƙarfe 12:15 na rana, aka shigar da ƙara cewar wata mota fara ƙirar Toyota Hilux (mai lamba GWA 845 CY), an sace ta mahaɗar Karji, amma daga bisani an ganta a otal ɗin Yazid da ke kan titin Ali Akilu a Kaduna.

Kakakin ya ce a ranar Laraba, DPO ɗin ofishin ’yan sanda na Millennium City, ya samu rahoton zirga-zirgar wasu da ake zargin masu laifi ne a ƙauyen Maraban Rido.

Sakamakon haka, sun kama wasu mutum uku ɗauke da makamai a kan babur.

Ya ce waɗanda ake zargin na ɗauke da wasu bindigu da harsasai.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan waɗanda ake zargin.

Hassan, ya ce Kwamishinan ’yan sandan Kaduna, Mista Ali Dabigi, ya tabbatar da cewa rundunar ta ci gaba da jajircewa wajen kiyaye tsaro da dukiyoyin al’ummar jihar.

Ya kuma yaba da haɗin kan da jama’a ke bai wa rundunar a jihar.

Tsofaffin ma’aikatan Gombe 2,204 sun karɓi giratuti N4.2bn

Bam ya yi ajalin ɗaliban Islamiyya 2 a Abuja 

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Saudiyya

’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra