’Yan sanda sun kama ɗan bindiga, sun kwato AK-47 a Kaduna 

‘Yan sandan sun kwato bindiga kirar AK-47 a hannun wanda ake zargin.

’Yan sanda sun kama ɗan bindiga, sun kwato AK-47 a Kaduna 

‘Yan Sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama wani da ake zargin dan bindiga ne tare da kwato bindiga kirar AK-47 a jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ne, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Jihar.

Hassan, ya ce jami’an rundunar sun samu bayanan sirri da ya kai ga cafke wanda ake zargin a ranar 12 ga watan Fabrairu.

“Wanda ake zargin, Adamu Shuaibu mazaunin kauyen Dumale a Karamar Hukumar Kagarko a jihar, an same shi da bindiga kirar AK-47 a lokacin da aka kama shi a ranar 12 ga watan Fabrairu.”

A cewarsa, wanda ake zargin na ɗaya daga cikin maharan da suka addabi kauyen Jere da ke Karamar Hukumar Kagarko a jihar.

Ya kara da cewa za su gurfanar da shi a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

Hassan, ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Audu Ali, ya yaba wa jami’an rundunar kan nasarar kama dan bindigar.

Ya kuma lashi takobin ci gaba da yakar masu aikata laifuka a jihar.

Ya bukaci mazauna jihar da su bai wa ‘yan sanda sahihin bayanai domin samun damar kare rayuka da dukiyoyinsu.

’Yan Bindiga: An miƙa wa gwamnatin Kaduna mutum 58 da aka ceto

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna

Barikin Ladi: Asalin garin da yanayin rayuwar mazauna