’Yan sanda sun kama ɗan bindiga, sun kwato makamai a Kaduna
‘Yan sandan sun cafke wanda ake zargin a wani samame da suka kai.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama wani mutum mai shekara 35 da ake zargi da satar mutane a jihar.
Rundunar ta kuma kwato makamai da alburusai a wani samame da ta kai a gidan wanda ake zargin a jihar.
- Mahara sun sace shugaban jam’iyyar PDP na Edo
- An shiga farautar ɓata-garin da suka kashe sojoji 16 a Delta
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan, ya fitar ranar Juma’a a Kaduna.
ASP Hassan ya ce rundunar ta kama wanda ake zargin ne a ranar 29 ga watan Fabarairu a gidansa da ke ƙauyen Ganga Uku a Mararrabar Jos.
Ya ce jami’an ’yan sandan sun kwato kananan bindigogi guda biyu, harsashi da sauransu.
Kakakin ya ce mutumin da ke hannu ana zarginsa da haɗa baki da wasu da suka yi garkuwa da wani mai suna Sama’ila Abdullahu mai shekaru 40 a garon Keke na jihar a ranar 13 watan Fabrairu.
Ya ce wanda ake zargin yanzu haka yana tsare kuma “wannan nasarar da aka samu na ƙara jaddada ƙudirin rundunar ‘yan sanda karkashin jagorancin Kwamishinan ’yan sanda, Mista Ali Dabigi C na tabbatar da doka da oda a Jihar Kaduna.”