’Yan sanda sun kama baƙin haure 165 a Kebbi
Rundunar ta miƙa su ga Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa don gudanar da bincike.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, ta kama wasu mutum 165 da suka shigo Najeriya ba tare da izini ba.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Nafi’u Abubakar, ya ce an kama mutanen ne a Birnin Kebbi.
Ya ce 35 daga cikinsu ’yan asalin ƙasar Burkina Faso ne, yayin da 11 ’yan asalin Jamhuriyar Benin ne.
Akwai kuma mutum biyar daga Nijar, huɗu daga Mali, sai mutum 110 ’yan ƙasar Ivory Coast.
Ya ce mutanen ba su da takardun izinin shigowa Najeriya kuma an same su da aikata damfara.
Rundunar ta bayyana cewa an miƙa su ga Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa da ke Jihar Kebbi, domin gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakin da ya dace.