’Yan sanda sun kama barayin mota a Nasarawa
Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ta gano tare da kwato wata sabuwar mota kirar Toyota Camry da wasu ’yan fashi da makami suka sace a garin Karu da ke jihar. Kakakin Rundunar ASP Usman Numan Isma’il ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da motar ga manema labarai a ofishin rundunar da ke […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ta gano tare da kwato wata sabuwar mota kirar Toyota Camry da wasu ’yan fashi da makami suka sace a garin Karu da ke jihar.
Kakakin Rundunar ASP Usman Numan Isma’il ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da motar ga manema labarai a ofishin rundunar da ke Lafiya.
Ya ce ’yan sandan da ke sintiri a yankin tare da hadin gwiwar wasu ’yan banga a karkashin jagorancin sanannen mai kama barayin nan Alhaji Ali kwara ne suka hangi motar da aka ajiye a kan babbar hanyar Keffi zuwa Abuja a garin Karshi.
Ya ce da ’yan fashin da ke cikin motar suka hangi ’yan sandan sai suka bude musu wuta inda su da ’yan bangar suka mayar da wuta daga bisani daya daga cikin barayin ya samu mummunan rauni sauran kuma suka tsere zuwa cikin daji.
Motar mai lambar DC 278 ABC a cewar DSP Usman, an kwato ta tare da wata bindiga kirar AK47 da harsasai 27 da karamar bindiga daya da bindigar harba-ka-ruga daya da abin buga hatimi da lambobin mota biyu da Naira dubu 100 da sauransu.
Ya ce dan fashin da ya samu rauni yayin artabun ya rasu a hanya a lokacin da ake kokarin kai shi asibiti, inda aka ajiye gawarsa a dakin adana gawarwaki na Asibitin kwwarru na dalhatu Araf da ke Lafiya.
Ya ce an gano motar ta wani mai suna Barista Henry Tawo Ebu ne wanda ya kai rahoton yi masa fashinta ga ofishin ’yan sanda na Mararaba. Ya ce, mafasan sun shiga gidansa da ke unguwar Greater Tomorrow a Karu da daddare inda suka yi amfani da bindiga suka kwace masa motar.