’Yan sanda sun kama dan kungiyar asirin da suka dade suna nema

Wani babban ɗan ƙungiyar asiri da rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta ɗana wa tarko fiye da shekara 3 ya shiga komarta a ranar Lahadin da ta gabata. An kama dan ƙungiyar asirin mai suna Micheal Agbeyangi, wanda ake wa laƙabi da Alhaji Godonu a ranar Lahadin da ta gabata, a maɓoyarsa da ke Ado-Odo […]

’Yan sanda sun kama dan kungiyar asirin da suka dade suna nema

Wani babban ɗan ƙungiyar asiri da rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta ɗana wa tarko fiye da shekara 3 ya shiga komarta a ranar Lahadin da ta gabata.

An kama dan ƙungiyar asirin mai suna Micheal Agbeyangi, wanda ake wa laƙabi da Alhaji Godonu a ranar Lahadin da ta gabata, a maɓoyarsa da ke Ado-Odo a jihar, a sakamakon bayanan sirri da rundunar ’yan sandan shiyar Owode-Ebgbado ta samu game da shi.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ’yan sandan ta daɗe tana neman ƙasurgumin ɗan ƙungiyar asirin ruwa a jallo, wanda ake tuhuma da aikata muggan laifuka da tayar da hankalin jama’ar jihar, lamarin da ya yi sanadiyyar salwantar rayukan jama’a da dama. “A lokacin da rundurmu ta yi masa kwantan ɓauna a maɓoyarsa, an kama shi da gatari da takobi da wasu nau’in kayayyakin asiri na tsatsibanci” inji shi.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ogun, Ahmad Iliyasi ya ba da umarni a mika ƙasurgumin ɗan ƙungiyar asirin zuwa sashen hana muggan laifukan da suka shafi garkuwa da jama’a da muggan ayyukan ƙungiyoyin asiri, domin ci gaba da bincike.