’Yan sanda sun kama dillaliyar jariri

Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta samu kama wata mata mai suna Talatu Dauda mai kimanin shekara 37 a duniya wanda ta fito daga Jihar Filato bisa zarginta da sace wani yaro dan shekara daya da wata biyar wanda ta sayar da shi a kan Naira dubu 200.Ana zargin Talatu da sayar da yaron ga […]

’Yan sanda sun kama dillaliyar jariri
’Yan sanda sun kama dillaliyar jariri

Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta samu kama wata mata mai suna Talatu Dauda mai kimanin shekara 37 a duniya wanda ta fito daga Jihar Filato bisa zarginta da sace wani yaro dan shekara daya da wata biyar wanda ta sayar da shi a kan Naira dubu 200.
Ana zargin Talatu da sayar da yaron ga wata mace mai suna Ann-Okechuku mai kimanin shekara 50 a wadda take zaune a Jihar Enugu da ke kudancin Najeriya, wadda ita ma ta sayar da yaron ga wata mata mai suna Hannah Ashaku mai kimanin shekara 41 ’yar asalin Jihar Benuwai.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi DSP Haruna Muhammed ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba ga manema labarai a Bauchi. Ya ce dukkan wadanda ake zargin suna hannun rundunarsu ta Jihar Bauchi kuma suna ci gaba da ba da bayanai, da zarar an kammala bincike za a gufanar da su a gaban kotu.
Da take zantawa da wakilin Aminiya, mahaifiyar yaron Ramatu Musa ta ce tana zaune a cikin gida sai Talatu Dauda ta zo ta dauki Muhammadu Najasi ta gudu da shi, inda ta sayar da shi a kan Naira dubu 200 ga wata mata a Kudu.
Ta ce “Muhammadu ya shafe sama da kwana 20 a hannun wadda ta sace shi da wadda ta saye shi. Kuma lokacin da abin ya faru ni da mahaifinsa mun kai rahoto ga ’yan sanda a Bauchi daga bisani sai muka samu labarin cewa an sayar da yaron, amma an kama Talatu Dauda tana hannu, mun tafi da ’yan sanda daga nan Bauchi zuwa garin Enugu kuma an samu nasarar kamaTalatu tare da mata biyu, wannan shi ne abin da zan fada a takaice.”
Ta ce sun dauki tsawon lokaci suna neman Talatu Dauda kafin su samu labarin cewa ta jima tana safarar jarirai daga Bauchi zuwa kudancin kasar nan. “Wannan abin da ya faru ya zamo min darasi, kuma daga yanzu babu wanda zan sake amincewa da ita in ba ta dana ta rike. Lokacin da aka gudu da Muhammadu Najasi akwai mutane da dama da suka yi ta yada jita-jitar cewa wai na sayar da dana ne, kafin Allah Ya bayyana gaskiyar abin da ya faru. Ina godiya ga Allah, sannan ina mika godiya ga Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi da sauran al’umma da suka taimaka mana da addu’o’i har Allah Ya tona asirin Talatu da wadanda ta sayar musu da shi,” inji ta.