’Yan sanda sun kama direban da ke yawo da kwarangwal a matsayin fasinja

Jami’an ’yan sandan Jihar Arizona da ke Amurka sun kama wani tsoho mai kimanin shekara 62, mai suna Alas wanda ya shirya wani kwarangwal na roba ya daure shi da igiya a kujerar baya ta motarsa yana tukawa a matsayin fasinja. Mutumin ya shirya kwarangwal din tsaf a kujerar fasinja, bayan dakatar da shi jami’an […]

’Yan sanda sun kama direban da ke yawo da kwarangwal a matsayin fasinja

Jami’an ’yan sandan Jihar Arizona da ke Amurka sun kama wani tsoho mai kimanin shekara 62, mai suna Alas wanda ya shirya wani kwarangwal na roba ya daure shi da igiya a kujerar baya ta motarsa yana tukawa a matsayin fasinja.

Mutumin ya shirya kwarangwal din tsaf a kujerar fasinja, bayan dakatar da shi jami’an suka yi inda suka ci tararsa.

Kwarangwal din robar an shirya shi ne ta yadda duk wanda ya gan shi zai razana, kuma an sanya masa sutura kamar mutum mai rai, inda aka dora masa hula a kai, sannan a tsakanin kafafunsa an rayata masa wani akwati tare da daure shi da wata igiya ta yadda zai zauna da kyau. Jami’an sun gano mutumin mai suna Alas yana da lasisin tukin mota.

Jami’an kare jama’a na Arizona, sun wallafa a shafinsu na tiwita cewa: “Kana tunani don ka mallaki lasisin tuki za ka iya yin tuki tare da kwarangwal ne? Ka aikata laifi!”

Wannan lasisin tukin ta HOB ana amfani da ita ce lokacin da ake samun cinkoson motoci da fasinjoji a cikin mota.

Jami’an Arizona sun ce, ana samun sama da direbobi dubu 7 da suke yin watsi da dokokin tuki duk shekara a jihar.