‘Yan sanda sun kama direban da ya dauki bajimi a kujerar fasinja

Lee Meyer mazaunin garin Neligh—yana tuki tare da bajimi mai suna Howdy Doody, a kowace hanyar.

‘Yan sanda sun kama direban da ya dauki bajimi a kujerar fasinja

Jami’an ’yan sanda sun kama wani direba mai suna Lee Meyer saboda daukar bajimi a kujerar fasinja ta gaba wadda aka kebe don dan Adam.

Bajimin nau’in Watusi mai girman kaho ’yan sandan birnin Norfolk a Gundumar Nebraska da ke Amurka ne suka kama direban bayan samun korafin da aka yi musu game da bajimin da mutumin ya dauka, in ji kafar labarai ta News Channel Nebraska.

Lee Meyer mazaunin garin Neligh—yana tuki tare da bajimi mai suna Howdy Doody, a kowace hanyar.

Hukumomin da suke kula da hanyoyi a yau da kullun kuma sun ga alama mai launin rawaya a gefen motar bayan sun duba sai ga bajimin a ciki.

“Jami’an sun samu kiran waya da ke nuna wata mota na shiga garin tare da saniya,” kamar yadda Kyaftin din ’Yan sanda Chad Reiman ya shaida wa tashar.

“Sun yi tunanin cewa zai zama dan maraki ne, ko wani karamin dabba ko wani abu da zai shiga cikin motar.

“Sakamakon haka, jami’in ya umarci jami’in da ke kula da hanyar ya dakatar da motar saboda dalilin tsaro,” in ji Reiman.

Reiman ya ci gaba da cewa, “Akwai wasu batutuwa masu muhimmanci game da wannan hali.

Jami’in ya zabi ya rubuta masa gargadi kuma ya roke shi ya dauki bajimin ya koma gida ya bar birnin.

“Ban san dalilin da ya sa yake yin hakan ba a ranar,” Reiman ya bayyana wa kafar labarai ta People.com

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta