’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina
Rundunar ta kuma ƙwato makamai da motocin da suke aikata laifukan da su.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta cafke wasu gungun ’yan fashi da makami, da suka addabi matafiya a kan titin Kano zuwa Zariya.
’Yan fashin suna kafa shinge da duwatsu a kan hanyar, inda suke tare motoci tare da yi wa fasinjoji ƙwace.
- ’Yan sanda sun kama mai yi wa ’yan bindiga safarar makamai a Kaduna
- Zaɓen Edo: INEC ta tsawaita kaɗa ƙuri’a a wasu yankuna
Bayan cafke su, rundunar ta yi nasarar ƙwato kayan sata da darajarsu ta kai kimanin Naira miliyan huɗu, ciki har da buhunan atamfofi da leshi guda 94.
An kama waɗanda ake zargin ne a ranar 8 ga watan Satumba, 2024, bayan samun wasu bayanan sirri da jami’an tsaro suka yi a Funtuwa.
An gano kayan sata, da suka haɗar hatsi da man girki, sannan an ƙwato motocin wasu motoci ƙirar Volkswagen Golf III da Ford Focus da suke amfani da su wajen aikata laifuka.
A wani labarin kuma, ’yan sanda sun kama wasu mutum uku da bindiga da harsashi guda huɗu.
An kama su ne a ranar 28 ga watan Agusta, 2024, bayan wani bincike da aka gudanar ta hanyar wani rubutu da aka wallafa a kafar sada zumunta.
Kazalika, ’yan sanda sun kama wani riƙaƙƙen barawon babur da motoci, tare da ƙwato wata mota da ya sace.
Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike kan dukkanin masu laifukan da ta kama, kuma za ta gurfanar da su da zarar ta kammala bincike.