’Yan sanda sun kama kasurgumin dan fashi a Jigawa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta samu nasarar kama wani da ake zargin kasurgumin dan fashi  ne mai suna Muhammed Bello Gwamna wanda ake zargin ya kware wajen fashi da makami da kwacen babura da sayar da shanun sata da fasa shagunan mutane da sauransu a yankunan kananan hukumomin Dutse da Birnin Kudu. Kwamishinan ’Yan […]

’Yan sanda sun kama kasurgumin dan fashi a Jigawa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta samu nasarar kama wani da ake zargin kasurgumin dan fashi  ne mai suna Muhammed Bello Gwamna wanda ake zargin ya kware wajen fashi da makami da kwacen babura da sayar da shanun sata da fasa shagunan mutane da sauransu a yankunan kananan hukumomin Dutse da Birnin Kudu.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Jigawa Alhaji Bala Zama Senchi ne ya sanar da taron manema labarai haka a ofishinsa da ke Dutse a ranar Talatar da ta wuce.

Ya ce wanda ake zargin da bakinsa ya amsa aikata laifin fashi da makami a wurare da dama ciki har da kauyukan Madobi da Baranda da Wurma da wasu kauyuka a kananan hukumomin Birnin Kudu da Takai da kuma garin Kafin Lemo a Jihar Kano.

Sannan ya fallasa abokan da suke sata tare da mutanen da suke sayarwa kayayyakin satar.

Kwamishinan ya kara da cewa, tuni rundunarsa ta kamo wadansu daga cikin masu sayen kayan satar da kuma abokan Mohammed wajen tafka ta’asar yayin da wadansu suka tsere.

Da yake yi wa manema labarai bayani, Mohammed Bello ya ce shi ba ya yin fashi da makami kuma shanun da aka ce satarsu ya yi, shanun mahaifinsa ne ya sayar.  Ya ce masu adawa da shi ne suka baza jita-jitar yana satar shanu da kuma yin fashi da makami ganin yadda ’yan mata suke rububi a kansa saboda irin farin jinin da yake da shi.

Daya daga cikin wadanda aka kama bisa zargin sayen kayan sata a wajen Mohammed mai suna Hamza Garba ya ce kimanin shekara hudu ke nan da ya sayi wasu tumaki a wajen Mohammed Bello amma sai yanzu aka ce na sata ne. Amma a wancan lokaci bai san Gwamna ya sato tumakin ba ne.

Sai dai Mohammed Bello da ake wa lakabi da Gwamna, ya yi alkawarin ba zai sake aikata sata a rayuwarsa ba idan aka sake shi.

Kwamishina Bala Zama Senchi ya ce za su gurfanar da wadanda aka kama a kotu da zarar sun kammala bincike don su fuskanci hukunci.