’Yan sanda sun kama magidanci kan fyade ga karamar yarinya

’Yan sandan a garim Shuwarin da ke karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa sun kama wani magidanci mai shekara 32 mai suna danlami Audu wanda aka fi sani da danlami Mai Kayan Miya da ke garin Shuwarin bisa zarginsa da yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyade. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, SP […]

’Yan sanda sun kama magidanci kan fyade ga karamar yarinya

’Yan sandan a garim Shuwarin da ke karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa sun kama wani magidanci mai shekara 32 mai suna danlami Audu wanda aka fi sani da danlami Mai Kayan Miya da ke garin Shuwarin bisa zarginsa da yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyade.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, SP Audu Jinjiri wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce tuni ’yan sanda suka kama mutumin yana amsa tambayoyi da zarar sun kammala za su mika shi ga sashin zurfafa bincike na rundunar domin yin gwaje-gwaje a kan yarinyar kafin gabatar da shi a gaban kotu.

Yarinyar wadda aka sakaye sunanta, ita ce da kanta ta shaida wa mahaifiyarta halin da ake ciki, iyayen suka gabatar da kuka ga mai unguwarsu yayin da wani abokin mahaifinta mai suna Hassan dan sanda ya gabatar da korafi ga ofishin ’yan sandan Shuwarin suka kama shi.

Yarinyar ta ce danlami Mai Kayan Miya ya yi mata barazana da wuka ewa zai kashe ta idan ta yi masa ihu ko ta tona masa asiri wani ya ji, inda ya yi amfani da karfi wajen yi mata fyade tare da rufe mata baki.

 Yarinyar ta ce, wanda ake zargin ya jima yana tarkon yadda zai yi lalata da ita amma ba ta amince ba, sakamakon haka ne ya bi ta daji lokacin da mahaifiyarta ta aike ta wani kauyen Majiyawa da ke kusa da Shuwarin, inda ya ce ta hau babur dinsa ya rage mata hanya zuwa inda za ta je, amma ta ce ba za ta hau ba shi ne ya yaudare ta cewa mahaifinta dan uwansa ne na jini don haka ba zai cutar da ita ba.

Ta ce bayan ta amince ta hau babur din ne suna cikin tafiya a cikin daji sai ta ga ya saki hanya ya fada cikin wani burtali, inda ya ce mata zai yi fitsari, kuma bayan ya gama fitsarin ne ya taso ya zaro wukake daga cikin aljihunsa ya ce mata ga abin da zai yi da ita kuma idan ta yi masa ihu zai yanka ta a karshe ya rufe mata baki ya kayar da ita ya yi mata fyade.

Ta ce da ta dawo gida ne ta kwashe lamarin ta shaida wa mahaifiyarta ita kuma ta shaida wa magabata har aka kai shi wurin ’yan sanda.

Jama’ar gari ciki har da ’yan uwan danlami Mai Kayan Miya suna zarginsa da cewa ya jima yana aikata badala da kanana yara wani lokaci da zawarawa da matan aure, a wasu lokuta ma yakan shiga gidajen makota ana fafararsa.

Wani daga cikin mutanen garin da aka sakaye sunansa, ya ce bayanan sirri sun nuna su danlami suna da wata kungiya a garin na Shuwarin da suke lalata ’ya’yan mutane,  sai dai sun ce kama shi a yanzu zai sa sauran su shiga cikin taitayinsu.