’Yan sanda sun kama masu algus din takin zamani a Gombe
Dubun masu yin algus din takin zamanin ta cika bayan sun sayar da na N540,000 an kai gona za a sa
Masu yin algus ta hanyar cudanya takin zamani da kasa suna sayar wa manoma a sun shiga hannu a Jihar Gombe.
Rundunar ’yan sandan jihar ta gurfanar da mutanen su uku da lam laifin yin algus na cudanya takin zamani da kasa suna sayar wa manoma a jihar.
Wadanda ake zargin su ne Saleh Sahabi masu shekaru 39 zuwa 40 dukkansu mazauna Karamar Hukumar Yamaltu Deba a jihar Gombe.
Da yake gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar ’yan sandan jihar, kakakin rundunar, ASP Buhari Abdullahi, ya ce a ranar 8 ga watan Yuli, 2024 ’yan sanda sun samu korafi daga wasu mazauna garin Kumo cewa sun sayi buhu 27 na takin NPK Golden akan kudi N540,000 daga wajen wadanda ake zargin.
A cewarsa wadanda suka sayi takin suna isa gonakinsusu don yin amfani da takin, sai suka gano cewa ƙasa ce gauraye.
Buhari Abdullahi, ya kara da cewa, a yayin bincikensu, wadanda ake zargin sun amsa laifin.
Sun kuma ambaci wani mai suna Shehu Shagari da ake kira Nachilo a garin Gombe a matsayin wanda ya sayar musu da takin.
Ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala binciken.