’Yan sanda sun kama masu fasa bututun mai a ibadan

Rundunar ’yan sanda a Jihar Oyo ta gano wani kungurmin daji da ake fasa bututun man fetur tare da boyewa cikin durum-durom masu yawa, ana sayarwa da tsadar gaske ta haramtacciyar hanya ga mabukata. Mutane uku da aka kama da hannu a kan wannan al’amari sun ambaci wani mutum mai suna Koste da suka ce […]

’Yan sanda sun kama masu fasa bututun mai a ibadan
’Yan sanda sun kama masu fasa bututun mai a ibadan

Rundunar ’yan sanda a Jihar Oyo ta gano wani kungurmin daji da ake fasa bututun man fetur tare da boyewa cikin durum-durom masu yawa, ana sayarwa da tsadar gaske ta haramtacciyar hanya ga mabukata.

Mutane uku da aka kama da hannu a kan wannan al’amari sun ambaci wani mutum mai suna Koste da suka ce yana aiki a kamfanin NNPC da yake taimaka musu cikin sirri. Haka kuma ’yan sandan sun kama manajan gidan sayar da man fetur na Patkan da ke Ibadan, Mista Tunde Oyebamiji a dalilin sayen sataccen bakin mai lita dubu 31 daga hannun barayin da suka yi fashin tankar mai a kan hanyar Legas zuwa Ilorin. Akwai mutane 4 da mace a cikinsu da aka kama da ake zargin su da hannu wajen yin amfani da makamai da kakin soja suka kwace tankar mai daga hannun direban da suka daure shi tare da karkatar da akalar motar bayan sun kwashe man da ke cikinta.
Da yake zagayawa da ’yan jarida cikin wannan daji tare da nuna musu gidan sayar da man fetur na Patkan, Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Muhammad Musa Katsina wanda ya jagoranci tawagar manyan jami’ansa ya ce, salon aikin hadin gwiwa a tsakaninsu da jama’a farar hula shi ya taimaka wa rundunar ta yi nasarar bankado kungurmin dajin da kama wadannan mutane masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa.
Ya ce: “Dukkanku kuna sane da halin da kasa ke ciki a kan matsalar karancin man fetur, wanda irin wadannan mutane marasa imani suke haifarwa. Wannan daji yana daga cikin manyan hanyoyin da miyagun mutane suke amfani da da shi wajen hana jama’ar kasa samun wadataccen mai da yi wa Gwamnatin Tarayya illa.”
Da yake tabbatar da cewa, a yanzu zai mayar da hankali ne wajen ganin an yi maganin bullar irin wadannan mutane a jihar, kwamishinan ya nemi jama’ar kasa masu kishi da su ci gaba da taimaka wa ’yan sanda wajen basu labarin bullar miyagun iri domin yin maganinsu.
Daga bisani kwamishinan ya nuna wa ’yan jarida manajan gidan mai na Patkan, wanda aka same shi da laifin sayen sataccen bakin mai lita dubu 31 daga hannun ’yan fashi da makami. Ya kara da cewa mutane 4 aka kama da ake zargin su da hannu wajen sanya kakin soja da yin amfani da bindigogi da suka makure direban da ke tuka motar tankar mai, suka jefa shi cikin daji da karkata akalar motar zuwa Ibadan; a inda suka tsiyaye bakin mai lita dubu 31 a cikin bututun karkashin kasa na wannan gidan mai suka jefar da motar a kan hanyar Legas zuwa Ibadan. Ya ce bayan direban ya samu kubuta ne ya kai rahoto ga ’yan sanda, suka hanzarta daukar matakin da ya kai su ga bankado wannan al’amari.