’Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane a Kano
’Yan sanda a Jihar Kano sun kama wadansu matasa uku bisa zarginsu da yin garkuwa da wani yaro mai kimanin shekara hudu, mai suna Al’amin Mustapaha tare da neman kudin fansa daga mahaifinsa. Mutanen da ake zargin sun hada da Idris Ibrahim da ke Unguwar G/Dutse da Idris Ibrahim mai kimanin shekara 19 da Khalid […]

’Yan sanda a Jihar Kano sun kama wadansu matasa uku bisa zarginsu da yin garkuwa da wani yaro mai kimanin shekara hudu, mai suna Al’amin Mustapaha tare da neman kudin fansa daga mahaifinsa.
Mutanen da ake zargin sun hada da Idris Ibrahim da ke Unguwar G/Dutse da Idris Ibrahim mai kimanin shekara 19 da Khalid AbdulRahman mai kimanin shekara 24, wadanda mazaunin Unguwar Dabai ne, sai kuma Ahmad Ibrahim Usman na Unguwar Aisami, mai kimanin shekara 20.
Kakakin Hukumar ’Yan sandan Jihar Kano, SP Magaji Musa Majiya ya shaida wa manema labarai cewa wadanda ake zargin sun dauke yaron ne a daidai lokacin da ya fito kofar gidansu, inda suka kira mahaifinsa a waya tare da bayyana masa cewa sai ya biya Naira dubu 100 kafin a sakar masa dansa.
Majiya ya ce, “Hakan ya sa mahaifin yaron ya yi gaggwar sanar da ’yan sanda halin da ake ciki, kasancewar suna da masaniya game da bacewar yaron. Bayan sanar da mu kasancewar muna da sashe da ke kula da wannan al’amari, karkashin jagorancinsu suka yi gaggawar daukar matakan da suka kamata ta hanyar amfani da kayayyakin bincike na zamani, suka gano inda masu garkuwa da mutanen suke har suka yi nasarar kama su tare da karbo yaron ba tare da rauni ko biyan kudin fansa ba.”
Majiya ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.
Mahaifin yaron ya bayyana yadda al’amarin ya faru, inda ya ce “Lokacin da muka duba dukan wurare a unguwarmu da makwabtanmu, sai na kai rahoton bacewarsa ga ’yan sanda. Daga baya kuma sai ga kiran waya, inda suka nemi in biya Naira dubu 100 a matsayin kudin fansar yaron. Bayana na sanar da ’yan sanda ne suka ceto yaron cikin koshin lafiya. Na gode kwarai da gaske.”
Yayin da yake zantawa da manema labarai, daya daga cikin wadanda ake zargin wanda kuma shi ya shirya al’amarin, Idris Ibrahim ya ce talauci ne ya kai su ga aikata haka, kasancewar yana son idan ya samu kudin ya je ya sayi sutura. “Na shirya haka ne don in samu kudin da zan sayi sutura, gaskiya ba ni da halin yin dinki, kasancewar iyayena sun rasu; ga shi kuma ba na yin wata sana’a,” inji shi.