’Yan sanda sun kama masu hannu a kisan dan jarida

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Adamawa Audu Madaki ya ce sun kama mutum biyu da suke zargi da hannu wajen kisan wani dan jarida da aka yi a jihar a makon jiya. Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da Shugaban Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa (NUJ), Cif Chris Isiguzo ya kai […]

’Yan sanda sun kama masu hannu a kisan dan jarida
’Yan sanda sun kama masu hannu a kisan dan jarida

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Adamawa Audu Madaki ya ce sun kama mutum biyu da suke zargi da hannu wajen kisan wani dan jarida da aka yi a jihar a makon jiya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da Shugaban Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa (NUJ), Cif Chris Isiguzo ya kai masa ziyara domin ganin wadanda suka aikata wannan mugun aiki sun shiga hannu.

Madaki ya ce ’yan jarida da ’yan sanda abokan juna ne domin tare suke aiki don haka dole ne su ga sun kare kowane dan jarida a jihar domin samun ci gaba da zaman lafiya.

Cif Christ Isiguzo ya jinjina wa ’yan sandan game da irin kokarinsu, sannan ya bukaci su zage dantse don ganin an kama wadanda suka kashe Nashion Madwell.

“Ba ma shakka kan kwazon da ’yan sandan Najeriya ke da shi, domin su ne wadanda aka fi jinjinawa da iya aiki a Afirka baki daya, “inji shi.

Ya kara da cewa “Ina kira ga ’yan uwana ’yan jarida da ’yan sanda da a sake kulla zumunci domin wadannan ayyukan idan sun hada kai za a samu ci gaba da kuma zaman lafiya,” inji shi.

Marigayi Madwell dai yana aiki da gidan Rediyon Fombina FM ne da ke Jihar Adamawa har zuwa lokacin da wadansu suka kama shi suka kashe shi sannan suka yada gawarsa a kusa da ofishinsa na Fombina FM.