‘Yan sanda sun kama masu laifuka 220 a Kano
‘Yan sandan jihar Kano sun kama sama da mutum 220 da ake zargin masu aikata laifuka ne da suka hada da: fashi da makami, mu`amala da miyagun kwayoyi, mallakar muggan makamai da tada rikici da dai sauransu. Takwas daga cikin wadanda aka kama su ne suka yi wani fashi a wani kamfani da ke birnin […]
‘Yan sandan jihar Kano sun kama sama da mutum 220 da ake zargin masu aikata laifuka ne da suka hada da: fashi da makami, mu`amala da miyagun kwayoyi, mallakar muggan makamai da tada rikici da dai sauransu.
Takwas daga cikin wadanda aka kama su ne suka yi wani fashi a wani kamfani da ke birnin Kano, inda suka sace kwamfutocin Laptop shida da kwamutocin tebur biyu sai kuma talabijin bango inci 32.
Kakakin hukumar ‘yan sandan DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya gabatar da masu laifin a ofishin `yan sanda na unguwar Bompai a Kano.