’Yan sanda sun kama masu safarar bindigogi a Edo

Rundunar ta ce da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu.

’Yan sanda sun kama masu safarar bindigogi a Edo

Rundunar ’Yan sandan Jihar Edo, ta ce jami’anta sun kama wasu da ake zargin masu safarar bindigogi ne a jihar.

Kakakin rundunar, DSP Tijani Momoh ne, ya bayyana haka, inda ya ce Mataimakin Babban Sufeton ’Yan sanda mai kula da Shiyyar Edo da Delta, Mista Arungwa Nwazue ne, ya bayar da umarnin yin bincike.

Ya ce sun gano miyagun makamai a hannunsu yayin da zaɓen Gwamnan Jihar Edo ke ƙaratowa.

A ranar Juma’ar ne ’yan sandan suka kai samame ƙarƙashin jagorancin ASP Mohammed Usman, maɓoyar waɗanda ake zargin bayan samun bayanan sirri a garin Ileh da ke Ekpoma a Ƙaramar Hukumar Esan ta Yamma.

A yayin samamen, sun samu nasarar kama mutum biyu da ake zargin ’yan bindiga ne.

Kazalika, jami’an sun ƙwato bindigogi ƙirar gida guda 30 da kuma wani akwati da ke ɗauke da na’urar da ake amfani da ita wajen ƙera makamai.

Binciken farko da aka yi kan lamarin, ya nuna cewa waɗanda ake zargin suna sayarwa da ba da hayar bindigogin ga masu garkuwa da mutane da ’yan fashi.

Su kuma suna amfani da su wajen gudanar da miyagun ayyukansu a Jihar Edo da jihohi maƙwabta.

Rundunar ta bayar da umarnin yin cikakken bincike kan lamarin da kuma gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja