’Yan sanda sun kama masu sata a bankunan Adamawa
Yan sanda a Jihar Adamawa sun kama wasu mutum biyar da ake zargin cewa barayi ne da suke yawan yin sata a bankunan jihar.Akalla bankuna uku ne aka yi wa sata a makonni biyu da suka gabata, inda barayi suka shiga har cikin bankunan suka kwaci kudi a hannun masu zuwa banki da rana-tsaka.’Yan sanda […]
Yan sanda a Jihar Adamawa sun kama wasu mutum biyar da ake zargin cewa barayi ne da suke yawan yin sata a bankunan jihar.
Akalla bankuna uku ne aka yi wa sata a makonni biyu da suka gabata, inda barayi suka shiga har cikin bankunan suka kwaci kudi a hannun masu zuwa banki da rana-tsaka.
’Yan sanda sun ba da shawara ga mutanen jihar cewa su rika lura da kuma kula a duk lokacin da su ka je banki domin kada su fada hannun barayin.
Kakakin ’Yan sandan Jihar DSP Othman Abubakar ya ce “Muna sanar da jama’a game da yawan sata a bankuna a yanzu. Don haka, jama’a su rika lura da kula a duk lokacin da suke tafiya da al’amuransu a bankunan.”
DSP Abubakar ya ce barayin na amfani da wani makulli ne domin bude ababen hawan mutanen da suka je banki, inda ya ce barayin da aka kama sun yi musu bayani a kan yadda suke gudanar da aika-aikarsu.