’Yan sanda sun kama masu satar mutane a Adamawa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa ta kama wasu mutum hudu da ake zargi da satar mutane domin su amshi makudan kudi daga ’yan uwansu a matsayin fansa.Kakakin Rundunar ’Yan sandan DSP Othman Abubakar ya bayyana haka ne ga manema labarai, inda ya ce sun samu nasarar kama wadanda ake zargin ne da taimakon jama’a.Ya ce […]

’Yan sanda sun kama masu satar mutane a Adamawa
’Yan sanda sun kama masu satar mutane a Adamawa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa ta kama wasu mutum hudu da ake zargi da satar mutane domin su amshi makudan kudi daga ’yan uwansu a matsayin fansa.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan DSP Othman Abubakar ya bayyana haka ne ga manema labarai, inda ya ce sun samu nasarar kama wadanda ake zargin ne da taimakon jama’a.
Ya ce sun kama mutum hudu da ake zargi da sace Injiniya Wilson wanda kane ne ga tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Adamawa a karkashin Jam’iyyar SDP, Injiniya Markus Gundiri da dan majalisa Usman Adamu da ke wakiltar mazabar Ganye da Toungo da Alhaji Aminu Sarkin Tsabtar Adamawa, kuma an kama wadanda ake zargin dauke da bindigogin kirar AK47 da kuma harsassai 60.
Ya ce ’yan sanda sun fara bincike kan wadada ake zargin a sashin binciken manyan laifuffuka na rundunar ’yan sandan jihar (CID).
Kakakin ’yan sandan ya gode wa jama’a kan hadin kan da suka ba su don gano wadanda ake zargin, inda ya yi fatan za su ci gaba da ba su goyon baya da hadin kai domin harkar tsaro ta shafi kowa a jihar.