’Yan sanda sun kama masu yin fashi a gidajen mai

’Yan sanda a jihar Gombe sun kama mutum uku da suke zargi su ne suka addabi gidajen mai da fashi da makami suna kashe masu gadi suna kwashe kudi. An gabatar da ’yan fashin ne tare da wadansu mutum bakwai da ake zargin sun kware wajen tare hanya suna yin fashi da makami a yanki […]

’Yan sanda sun kama masu yin fashi a gidajen mai

’Yan sanda a jihar Gombe sun kama mutum uku da suke zargi su ne suka addabi gidajen mai da fashi da makami suna kashe masu gadi suna kwashe kudi. An gabatar da ’yan fashin ne tare da wadansu mutum bakwai da ake zargin sun kware wajen tare hanya suna yin fashi da makami a yanki Kuri kan hanyar Yamaltu-Deba.

Da yake gabatar wa manema labarai da wadanda ake zargin a hedkwatar ’yan sandan Gombe, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Austin Iwar, ya ce ’yan sanda sun samu labarin wadandaakr zargin batagarin ne ta hanyar bayanan sirri kuma ba ’yan asalin Jihar Gombe ba ne.

Kwamishinan ya ce masu fashi a gidajen mai din a lokacin artabunsu da ’yan sanda daya ya mutu biyu, kuma suna zuwa ne daga jihohin Sakkwato da Bauchi su kwana a otel da dare su shiga gidajen mai su kashe masu gadi su kwashe musu kudi.

Kwamishinan ya ce suna kokari su gano su wane ne iyayen gidansu a Gombe domin ba yadda za a yi su taso daga jihohin Sakkwato da Bauchi su hadu a Gombe su yi fashi ba tare da suna da iyayen gida ba.

Kwamishinan ya ce a cikin makonni shida kadai sun shiga gidajen mai biyar a fadar jihar suka kashe masu gadi uku suka yi gaba da kudade masu yawa wanda hakan ya daga wa al’ummar Gombe hankali musamman masu gidajen mai. “Mun same su da jabun katin shaida da ke nuna cewa su mambobin kungiyar Masu Harkar Man Fetur ne. Da muka yi bincike a wajen shugabannin kungiyar sai muka gano katin na jabu ne,” inji Kwamishinan.

Shugaban kungiyar Dillalan Man Fetur ta Jihar Gombe, Alhaji Bappah Muhammed, ya nuna farin ciki tare da godiya ga Allah kan wannan nasara da aka samu, sannan ya gode wa Kwamishinan ’Yan Sanda da jami’ansa kan wannan namijin kokari da suka yi.

Alhaji Bappah Muhammed ya tabbatar da cewa an kashe musu masu gadi uku, biyu a gidan mai na National da ke Tumfure daya a gidan mai na Arfat da ke hanyar zuwa Biu, wadansu kuma an ji musu munanan raunuka.

Gidajen man da suka fasa sun hada da MRS da OandO da Total da Arfat da ke hanyar Biu.

Mutanen da ake zargi da fashi a gidajen mai din su ne Ahmed Inuwa da ke Unguwar Bakaro a Bauchi sai Abdurrasheed Suleiman da ke Unguwar Mabera a Sakkwato.

Sauran bakwai da ake zargi da yin fashi a hanyar Yamaltu sun hada da Hamisu Adamu mai shekara 19 da Abdulra’uf Hamisu, shekara 27 da Sama’ila Bello 20 da Atiku Sa’idu 29 da Jamilu Ibrahim 26 da Ali Suleiman 20 sai Mustapha Ahmed 22. Kuma an kama su da makaman da suka hada da bindigogi adaka 2 da gatari 2 da karamar fistol kirar gida 1 da Arduna 2 da babur kirar Haojue 1 da wukake 2 da takobi 2 da jannareta 1.