‘Yan sanda sun kama mata 8 da laifin yawan banza

Jami’an ‘yan sanda sun gurfanar da wasu mata takwas a wata kotu dake unguwar Karshi Ariya 1 Abuja bisa laifin yawan banza a yankin Karu. Matan da aka kama sun haxa da Abraham Soye da Christabel Fripond da  Rejoice Jonah da Chidimma Onwigbo da Bella Isaac da Joy Sunday da Jennifer Mbamu da kuma Beauty […]

‘Yan sanda sun kama mata 8 da laifin yawan banza

‘Yan sandan Najeriya

Jami’an ‘yan sanda sun gurfanar da wasu mata takwas a wata kotu dake unguwar Karshi Ariya 1 Abuja bisa laifin yawan banza a yankin Karu.

Matan da aka kama sun haxa da Abraham Soye da Christabel Fripond da  Rejoice Jonah da Chidimma Onwigbo da Bella Isaac da Joy Sunday da Jennifer Mbamu da kuma Beauty David inda ake tuhumar su dai laifuka biyu wadanda suka hada da yawan banza da zaman kansu ba tare da kowa ba.

Wanda ya shigar da karar, Mahmud Lawal, ya bayyana wa kotun cewa an kama matan ne a ranar 9 ga wata Yuni 2018 lokacin da ayarin ‘yan sandan suke zagaya wa unguwanni karkashin jagorancin ASP Joseph wanda suke ofishin ‘yan sanda na Karu.