’Yan sanda sun kama Mataimakin Shugaban Malamai na kungiyar Izala

Wasu ’yan sanda da aka tabbatar sun zo a motar Operation Yaki sun kama Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Kaduna Malam Muhammad Bello Adam a safiyar ranar Juma’ar da ta gabata a gidansa da ke garin Saminaka. Uwargidan malamin Malama Khadijatu Abdullahi ta shaida wa wakilinmu […]

’Yan sanda sun kama Mataimakin Shugaban Malamai na kungiyar Izala
’Yan sanda sun kama Mataimakin Shugaban Malamai na kungiyar Izala

Wasu ’yan sanda da aka tabbatar sun zo a motar Operation Yaki sun kama Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen Jihar Kaduna Malam Muhammad Bello Adam a safiyar ranar Juma’ar da ta gabata a gidansa da ke garin Saminaka.

Uwargidan malamin Malama Khadijatu Abdullahi ta shaida wa wakilinmu cewa a ranar Juma’a bayan ya dawo daga sallar Asuba ya rubuta hudubar da zai yi a masallacin Juma’a, sai ya fita kofar gida kusan karfe 11:00 na rana. Ta ce ya bude kofar motarsa ya sa kafa zai shiga ke nan, sai ’yan sanda suka iso a mota, suka tambaye shi cewa shi ne Malam Bello? Ya ce shi ne, sai suka ce ya ba su wayarsa, da ya mika musu sai suka ce ya shiga motarsu suka tafi da shi.
Ta ce abin ya ba su mamaki domin malamin yana zaune da kowa lafiya a garin, “Mu hudu ne matansa kuma yana da ’ya’ya 25. Muna addu’ar Allah Ya fito da shi lafiya ba tare da an cutar da shi ba.”
Direban malamin, Malam Muhammad Sabi’u Hamza ya ce, “A ranar Malam ne ya yi mana limanci da wa’azi da Asuba kuma kusan karfe 11 na rana na fito kofar gida ana min aski, sai wani dana da muke tare, ya ce lafiya ga wata motar ’yan sanda nan ta zo unguwarmu. Sai na ce wa wanzamin ya sake ni, ina daga kai sai na ga motar ’yan sandan Hilud tsaye a kofar gidan Malam. Sun fito suna tsaye kowa rike da bindiga, sai na taho, na ga Malam yana kokarin shiga motar, kafin na isa sun daga sun tafi,” inji shi.
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’Yan sandan Jihar Kaduna, SP Aminu Lawan ya ce ba a tuntube sub a kafin a kama malamin. “Ba mu da masaniyar kama shi, kuma ba ya hannunmu, amma na samu labarin, su kansu ofishin ’yan sandan Saminaka sun ce ba ya hannunsu,” inji shi.