’Yan sanda sun kama matar da ta jefar da jaririnta a gefen hanya

Rundunar ta gurfanar da matar a gaban kotu kan karya dokar kare haƙƙin yara ta 2003.

’Yan sanda sun kama matar da ta jefar da jaririnta a gefen hanya

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja sun ceto wani jaririn kwana ɗaya da mahaifiyarsa, ta jefar a gefen hanya.

An samu jaririn a gefen hanya a bayan kasuwar Red Bricks da ke yankin Mpape, bayan ’yan sanda sun samu kiran gaggawa a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 10 na safe.

’Yan sandan sun yi saurin zuwa wajen, inda suka samu jaririn an naɗe shi cikin zani.

An kai jaririn Cibiyar Kula da Lafiya ta Mpape, inda likitoci suka tabbatar da cewa yana cikin ƙoshin lafiya.

Bayan gudanar da bincike, ’yan sanda sun kama mahaifiyar jaririn, Khadija Ali.

Matar ta amsa laifinta na jefar da jaririn, inda ta ce ta ɗauki matakin ne saboda ba za ta iya kula da jaririn ba, sakamakon mijinta ya guje ta.

Rundunar ta tabbatar wa da al’umma cewa za ta yi bincike tare da ci gaba da kare al’umma.

Rundunar ta ce za ta miƙa jaririn ga Ma’aikatar Kula da Al’amuran Matasa domin a kula da shi.

Sannan ta ce za ta gurfanar da mahaifiyar jariein a kotu bisa dokar Kare Haƙƙin Yara ta 2003.

’Yan sandan sun gode wa al’umma saboda haɗin kai da taimakon da suke ba su.

Sun kuma yi kira ga dukkanin mazauna birnin da su ci gaba da lura da al’amuran da ke faruwa da kuma sanar da ’yan sanda duk wani abu da ya shafi jama’a.

NAJERIYA A YAU: Amfanin Komawa Makaranta A Ranar Da Aka Bude Bayan Hutu

Tsofaffin ma’aikatan Gombe 2,204 sun karɓi giratuti N4.2bn

Bam ya yi ajalin ɗaliban Islamiyya 2 a Abuja 

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Saudiyya