’Yan sanda sun kama matasa 28 da ake zargi da addabar jama’ar Gombe
Sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe, Kudu Abdullahi Nma, ya ce jami’ansa sun kama matasa 28 da ake zargi da addabar jama’ar jihar. Kwamishinan ya bayyana haka ne ga manema labarai a ofishinsa mako guda da kama aiki a jihar.Kwamishinan ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ya tsarkake jihar daga […]
Sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Gombe, Kudu Abdullahi Nma, ya ce jami’ansa sun kama matasa 28 da ake zargi da addabar jama’ar jihar. Kwamishinan ya bayyana haka ne ga manema labarai a ofishinsa mako guda da kama aiki a jihar.
Kwamishinan ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ya tsarkake jihar daga barnar baragurbin matasan nan da suka kware a harkar Kalare suna kashe mutane da yi wa mata fyade da kwacen wayoyin hannu ga kuma sarar mutane da farfasa motocin da suka samu a bakin hanya.
Ya ce zai yi bakin kokarinsa wajen ganin ya dawowa al’ummar Gombe harkokin kasuwancinsu sun koma kamar yadda garin yake a can baya ta hanyar samar da kyakkyawan tsaro da kare dukiyoyi da rayukan jama’a.
Kwamishinan ya ce duk wuraren da ya samu labari nan gagararrun wurare ne daga zuwansa ya sa an aike da jami’ansa cikin farin kaya don samo rahoton da zai taimaka musu wajen kame batagari cikin sauki.
Malam Abdullahi Nma, ya ce kofarsa a bude take ga duk wanda mai zai taimaka da rahoton da zai sa a kama irin wadannan matasa saboda a samu wanzuwar zaman lafiya a ko’ina a jihar.
Daga nan sai yace za su bullo da wata hanya ta samun bayanai daga al’ummar garin ta hanyar samar da akwatunan ajiye wasiku a hedkwatar hukumar ko amfani da lambobin wayar salula.Ya ce da sun gama bincike za su tura matasan zuwa kotu don yanke musu hukunci.
Matasa da aka kama sun hada da wadanda ake zargi ’yan Kalare ne da sukayi kaurin suna a Unguwar Tudun Wada da ake kira ’yan B.Mobile cikinsu har da mata biyu.