’Yan sanda sun kama mawaƙi Naira Marley kan mutuwar Mohbad
An kama shi ne ranar Talata

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta kama mawakin nan Azeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley, bisa zarginsa da hannu a mutuwar mawaki Ilerioluwa Aloba (Mohbad).
Kakakin rundunar a Jihar, Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da daren Talata.
- Matasan Yobe sun yi zanga-zanga kan yawaitar fyade da satar mutane a Arewa
- DSS ta kama matashiyar da ta yi barazanar dasa wa su Kashim Shettima bam a Kano
“Azeez Fashola wanda aka fi sani da Naira Marley yanzu haka yana hannunmu muna yi masa tambayoyi da sauran bincike,” kamar yadda Benjamin ya wallafa a shafinsa na X (Twitter a da).
Bayan mutuwar ta Mohbad a ranar 12 ga watan Satumba dai an birne shi kashegari, an yi wa Naira Marley da Sam Larry da wasu saboda zarginsu da hannu a mutuwar tasa.
To sai dai Naira Marley ya nesanta kansa daga kowanne irin zargi da mutuwar tsohon yaron nasa a da, ya inda ya ce ba ma ya kasar lokacin da aka yi mutuwar.