’Yan sanda sun kama mijin amarya bayan wata biyar da kashe ta
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama mijin amaryar nan A’isha Isa Fagge da aka yi wa kisan gilla bayan kwana 12 da aurenta.An kama mijin amaryar Alhaji Nura Muhammad ne a harabar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Rijiyar Lemo ne bisa umarnin mai gabatar da kara Barista Lamido Abba Soron dinki.Barista Lamido Soron dinki […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama mijin amaryar nan A’isha Isa Fagge da aka yi wa kisan gilla bayan kwana 12 da aurenta.
An kama mijin amaryar Alhaji Nura Muhammad ne a harabar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Rijiyar Lemo ne bisa umarnin mai gabatar da kara Barista Lamido Abba Soron dinki.
Barista Lamido Soron dinki ya shaida wa Aminiya cewa bincike ya nuna mijin amaryar na daga cikin wadanda ake zargi da kisan marigayiyar.
“Akwai hujjoji karfafa game da zargin da ake yi wa mijin marigayiyar kan zargin sa hannunsa a cikin kisan matar tasa. Hakan ya sa na bayar da umarnin a kama shi,” inji shi.
Barista Soron dinki ya kara da cewa yana da shaidu guda uku da za su tabbatar da hakan a gaban kotu.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da kama mijin amaryar, inda ya ce yana sashin kula da manyan laifuffuka na rundunar.
Sai dai kafin ’yan sanda su tafi da Alhaji Nura ya ce yana shakkar Musuluncin duk wanda ya zarge shi da kisan amaryarsa. “Ta yaya hankali zai dauki cewa ni na kashe matata a daidai lokacin da muke amarci. Ban da haka ma laifin me ta yi min da zan kashe ta a wannan lokaci. Ina ganin akwai shakku a Musulunci duk wanda ya zarge ni da kisan matata. Na san cewa mutanen da ake zargi da kisanta tunda farko abokaina ne, amma wannan ba shi ne hujjar da za ta sa a zarge ni da hannu cikin kisan ba,” inji shi.
Tun farko an gabatar da Abdulzahir Muhammad da Rabi’u Abdulkadir a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Rijiyar Lemo inda ake zarginsu da laifuffukan laifin kisa da hadin baki wajen yin da kisan, laifukan da Barista Soron dinki ya ce sun saba wa sashi na 221 da 145 na kundin shari’a ta shekarar 2000.
Alhaji Nura wanda mai gabatar da karar ya gabatar a matsayin shaida ya bayyana wa kotu cewa abin da ya sani shi ne abokansa sun je gidansa a lokacin da ba ya nan, inda marigayiyar ta leko ta gaya musu cewa ba ya gida.
Alkalin kotun Mai shari’a Atiku Bello ya dage shari’ar zuwa ranar 11 ga Fabrairu. Idan za a iya tunawa a watan Agustan bara ne aka shiga gidan amarya A’isha a Unguwar Sharada Jaen aka yi mata kisan gilla.