’Yan sanda sun kama mutane 23 da laifuka daban-daban a Oyo

’Yan sanda a Jihar Oyo sun kama ma’aikatan kamfanin George Inbestment da ke Ibadan masu suna Olaronbi Saheed da Abdulkareem Yusuf da suka furta da bakinsu cewa su ne suka sace manyan motocin tifa guda 6 kirar SINO da kananan motoci 2 mallakar kamfanin da suke yi wa aiki. Sun ce sun sayar da motocin […]

’Yan sanda sun kama mutane 23 da laifuka daban-daban a Oyo

’Yan sanda a Jihar Oyo sun kama ma’aikatan kamfanin George Inbestment da ke Ibadan masu suna Olaronbi Saheed da Abdulkareem Yusuf da suka furta da bakinsu cewa su ne suka sace manyan motocin tifa guda 6 kirar SINO da kananan motoci 2 mallakar kamfanin da suke yi wa aiki.

Sun ce sun sayar da motocin ne ga Ibrahim Babankulu a Kaduna a kan Naira miliyan 20. Da yake nuna wadannan mutane da motocin da suka sace ga ’yan jarida a Ibadan, Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Oyo, Mista Abiodun Odude ya ce shugaban kamfanin George Inbestiment dan kasar Sin, Mista Wang Shou Bo, shi ne ya kai rahoton sace motocin ga ’yan sanda, wadanda suka yi nasarar kama ma’aikatan kamfanin su biyu. Ya ce bayan binciken kwakwaf ne mutanen suka ambaci sunan Ibrahim Babankulu, wanda shi ma aka kamo, bayan an gano duka motocin a hannunsa.

Haka kuma, kwamishinan ya nuna wani soja mai suna Kofur Akpan Edet, wanda ya jagoranci tawagar mutane 4 da suka yi fashin tankin mai dauke da lita dubu 40 na man fetur daga hannun direban motar da yaronsa da suka boye su a kauyen Omi-Adio bayan sun kwace masu kudade. Ya ce wannan sojan yana sanye da kakin soja a lokacin da ya jagoranci aikata danyen aikin.

Ya kuma nuna wata mata mai suna Alimat Kemi Mustapha, wadda aka taba korarta daga aikin dan sanda, a yanzu kuma aka kama ta sanye kayan aikin ’yan sanda da mukamin Sufeto da take yin amfani da su wajen tsoratar da mutane da karbar kudi masu yawa a hannunsu.

Sauran mutanen da aka kama har da wani mai suna Faruk Ibrahim, wanda ya fasa shagon ubangidansa da ake hada-hadar musayar kudade a Unguwar Sabo Ibadan ya sace kudi Naira miliyan 6 da dubu dari 2. A lokacin da ’yan jarida suka nemi jin ta bakinsa, Faruk mai shekaru 28 da haihuwa da matan aure 3 bai musanta laifin da ake tuhumarsa da aikatawa ba. An gano duka kudin a wani wuri da aka boye su a cikin gidansa.

Duka mutane 23 da ’yan sanda suka nuna wa ’yan jarida bayan kama su da aikata laifuka daban-daban a Jihar Oyo a tsakanin watannin Nuwamba da Disamba na shekarar da ta gabata, za a gurfanar da su gaban kotu ne da zarar an kammala bincike.