’Yan sanda sun kama mutum 2 da AK-47 a Zariya

Rundunar ta ce za ta gurfanar da su a kotu da zarar ta kammala bincike.

’Yan sanda sun kama mutum 2 da AK-47 a Zariya

Wasu ‘yan sanda a bakin aiki

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama wasu mutum biyu da suka ƙware wajen yin safarar makamai ga ’yan bindiga, tare da ceto wasu mutum biyu da aka sace.

Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Mansur Hassan, ya fitar a ranar Litinin.

Ya ce sashen da ke yaƙi da masu satar mutane na rundunar sun yi nasarar kama mutum biyu ɗauke da bindiga ƙirar AK-47 guda biyu a Madachi da ke yankin Zariya a kan hanyar Galadimawa.

Ya ce waɗanda ake zargin dukkaninsu mazauna Dogon Dawa ne a ƙaramar hukumar Birnin Gwari.

Ya ƙara da cewar waɗanda ake tuhumar, sun amsa aikata laifin, tare da bayyana cewar su ne suke yi wa ’yan ta’addar da suka addabi al’ummar yankin Zariya safarar makamai.

A cewarsa, bayanan da suka bayar ya taimaka wa rundunar da muhimman bayanai wanda rundunar ke amfani da su, don cafke ƙarin wasu.

Kakakin, ya ce rundunar tana gudanar da bincike a yanzu, kafin daga bisani ta gurfanar da su a kotu.