’Yan sanda sun kama mutum 40 kan samun su da hannu a ricikin Ombatse

Yan sanda a Jihar Nasarawa sun kama mutum 40 da suke zargi da hannu a cikin rikicin kabilanci da ya auku kwanan nan a garuruwan Assakio da Obi inda aka kashe mutane da dama aka kuma kone gidaje sama da 2,000. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Umaru Shehu ne ya bayyana haka a lokacin da yake […]

’Yan sanda sun kama mutum 40 kan samun su da hannu a ricikin Ombatse
’Yan sanda sun kama mutum 40 kan samun su da hannu a ricikin Ombatse

Yan sanda a Jihar Nasarawa sun kama mutum 40 da suke zargi da hannu a cikin rikicin kabilanci da ya auku kwanan nan a garuruwan Assakio da Obi inda aka kashe mutane da dama aka kuma kone gidaje sama da 2,000.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Umaru Shehu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga manema labarai kan halin da ake ciki game da tsaro a jihar a ranar Litinin da ta gabata.
Kwamishinan ’Yan sandan ya ce rundunar tana iya kokarinta domin maido da zaman lafiya a jihar baki daya. “A nata bangare Gwamnatin Tarayya ta kammala dukkan shirye-shirye na turo karin jami’an tsaro ciki har da sojoji a wuraren da rikicin ke ci gaba da aukuwa a jihar don kawo karshensa,” inji shi.
Da yake bayyani game da bacewar Babban Daraktan Bankin ’Yan sanda na kasa Alhaji Alhassan Gidado da Manajan Bankin na Abuja Tunde Banwo da direbansu a jihar lokacin rikicin, Umar Shehu ya ce an kama wadanda ake zargi da halaka mutanen kuma ’yan sanda sun gano inda suka binne gawarwarkinsu a wani daji a kauyen Adabu da ke jihar.
Kwamishinan ’Yan sandan ya bukaci mataimakinsa mai kula da sashin binciken manyan laifuffuka inda wadanda aka kama suke ya tabbatar sun fuskanci fushin doka.
Ya yi kira ga al’ummar jihar su rika kai rahotannin harkokin duk wadanda ba su amince da su ba ga hukumomin tsaro don taimaka musu wajen kawar da batagari daga jihar.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya rikicin kabilanci ya sake aukuwa a tsakanin al’ummar Alago da ke garuruwan Obi da Assakio da wasu mutanen Eggon, inda daga bisani ’yan kungiyar Ombatse suka shiga fadan suka yi ta kashe mutane da kuma kone gidaje sama da 2000 a garuruwan biyu.
Washegarin fadan ne jami’an bankin ’yan sanda suka bi hanyar Lafiya zuwa Obi don halartar daurin auren wani dan sanda inda wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka bude musu wuta a kauyen Adabu suka kashe su, suka kuma binne su da motarsu a wani daji a kauyen.