’Yan sanda sun kama mutum 5 da kayan layin dogo da aka sato a Yobe

Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike domin kama sauran da ke da hannu a lamarin.

’Yan sanda sun kama mutum 5 da kayan layin dogo da aka sato a Yobe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wasu mutum biyar da ake zargi da lalata da kuma satar kayayyakin layin dogo a jihar.

Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce an kama mutanen ne a ranar 5 ga watan Yuni, 2026, bayan wani samame da jami’an ’yan sanda suka gudanar tare da haɗin gwiwar ƙungiyar mafarauta a yankin Nannawaji da ke Ƙaramar Hukumar Gujba.

An kama waɗanda ake zargin ne a cikin wata mota ƙirar Mitsubishi Canter yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Potiskum ɗauke da ƙarafunan layin dogo guda 85 da ake zargin sun cire ba bisa ƙa’ida ba.

Bincike ya nuna cewa mutanen sun ambaci wani mutum mai suna Abba Chari, mazaunin Yadin Buni, a matsayin wanda ake zargin ya shirya aikin lalata layin dogon.

Rundunar ’yan sanda ta ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ke da hannu a lamarin tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Yobe, CP Usman Kanfani Jibrin, ya yi gargaɗi ga masu aikata laifuka da su daina lalata kadarorin gwamnati da sauran ayyukan da suka saɓa wa doka.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a ayyukan laifi.

Ga hotunan kayayyakin da aka samu a wajensu: