’Yan sanda sun kama mutum 575, sun ƙwato makamai a 2024 a Sakkwato
Rundunar ta jaddada aniyarta na ci gaba da kare al’ummar jihar.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, ta sanar da kama mutum sama da 575 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban tare da ƙwato makamai a shekarar 2024.
Kakakin rundunar, ASP Ahmad Rufa’i ne, ya bayyana hakan a ranar Laraba.
- ’Yan bindiga sun kashe ƙaramar yarinya da wasu mutum 2 a Kaduna
- Gwamnatin Kano ta yi watsi da dokokin haraji
Ya ce, cikin waɗanda aka kama, akwai mutum 51 da ake zargi da fashi da makami, 51 da ake zargi da satar mutane, da kuma mutum tara da ake zargi da aikata fyaɗe.
Haka kuma, an kama mutum 129 da ake zargi da kisa, 18 da yunƙurin kisa, 11 da suka ji wa mutane rauni, da mutum bakwai da aka kama bisa laifin aikata rashin ɗa’a.
Sauran waɗanda aka kama sun haɗa da mutum shida da ake zargi da ta’addanci, 90 da suka saci kaya, biyar da suka ɓalle gidaje, 39 da ana zargisu da damfara a Intanet.
Haka kuma an kama mutum 11 da suka karɓi kayan sata, 61 da suka lalata kaya, sai mutum takwas da aka kama da bindiga ba bisa ƙa’ida ba.
ASP Rufa’i, ya ƙara da cewa, an kuma kama mutum 17 bisa tayar hankalin jama’a, bakwai saboda laifukan da suka shafi bindiga.
Har ila yau, an kama mutum 31 bisa laifukan da suka shafi dukiya, da mutum 24 saboda laifukan da suka shafi mutane kai-tsaye.
Daga cikin kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindiga ƙirar GPMG guda ɗaya da harsasai guda shida, bindigogi AK-47 guda tara tare da harsasai 341.
Sauran sun haɗa da bindigogi AK-47 guda huɗu da aka ƙera a gida tare da harsasai biyu.
Hakazalika, akwai bindiga ƙaramar guda ɗaya, bindigar farauta ɗaya, motoci guda uku, tankar mai ɗaya, shanun sata 97, tumaki 29, jaki guda ɗaya, da mutum 27 da aka ceto.
Ya tabbatar wa al’umma cewa ’yan sanda sun ƙuduri aniyar tabbatar da tsaro da adalci a Jihar Sakkwato.
Sanata Wamako ya bai wa ’yan sanda kyautar motocin sintiri
A gefe guda kuma, Sanata Aliyu Wamakko, mai wakiltar Sokoto ta Arewa, ya bai wa ’yan sanda gudunmawar motocin sintiri guda 10.
Sanatan ya yaba wa ’yan sanda bisa ƙoƙarinsu na tabbatar da zaman lafiya a jihar, inda ya buƙaci su ci gaba da jajircewa.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Alhaji Ahmed Musa, ya gode wa sanatan bisa gudunmawar da ya ba su, inda ya ce hakan zai taimaka wajen inganta ayyukan yaƙi da laifuka a Jihar Sakkwato.