An kama su kan satar zinarin Naira miliyan 110 a Kebbi
Jami’in hukumar gidajen yari da aka kama ya amsa cewa shi ne ya sace zinare ta kimanin Naira miliyan 110 a Jihar Kebbi.
Wasu mutum shida sun shiga hannun ’yan sanda kan zargin satar zinari da kuɗinta ya haura Naira miliyan 109.5 a Jihar Kebbi.
Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sanda a jihar Kebbi na tuhumar su da sace sarkoƙin zinare guda biyar sauran kayan zinare daga wani gida a garin Ka’oje, Ƙaramar Hukumar Bagudo.
Sauran sun haɗa da zobba huɗu da munduwar hannu tara, da nauyinsu ya kai gram 782.7 — dukkansu mallakar ’ya’ya da ’yan uwar mai gidan.
Wanda ake tuhuma ya amsa laifi
Bayan samun koken, jami’an suka kama Ibrahim Abubakar Ka’oje, jami’i a Hukumar Gyaran Hali ta Kasa, wanda a yayin bincike, ya amsa laifin.
- ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
- ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
Ya bayyana cewa ya sayar da kayan ga wasu mutane biyu, dukkansu daga Sakkwato, tare da wasu mutum biyu a Jihar Kebbi.
An kuma gano wanda ya taimaka masa wajen sayar da wasu daga cikin kayan, inda ya karɓi naira miliyan 2.5 a matsayin lada.
Rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa har yanzu tana neman sauran da suka gudu, bisa zargin taimakawa wajen sayar da kayan sata.
Ana zargin an sayi filaye biyu a Birnin Kebbi da kuɗin da aka samu daga sayar da kayan.
Abubuwan da aka ƙwato
Kayan da aka ƙwato sun haɗa da munduwar hannu biyu, babur ɗin Haouje, da kuma wayoyin iPhone 16, Samsung Galaxy Ultra da Samsung Flip.
Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kebbi, Bello M. Sani, ya jinjina wa jajircewar jami’ansa bisa wannan nasara.
Ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da aiki tukuru domin cafke sauran da ake nema da kuma ƙwato dukkan kayan da suka rage.