’Yan sanda sun kama mutum 721, sun ƙwato motoci 13 a 2024 a Borno

Rundunar ta jadadda cewar za ta yi aiki da sabbin dabaru wajen daƙile aikata laifuka a jihar.

’Yan sanda sun kama mutum 721, sun ƙwato motoci 13 a 2024 a Borno

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta bayyana cewa ta kama mutum 721 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a shekarar 2024.

Waɗannan laifuka sun haɗa da fashi da makami, cin zarafin mata, garkuwa da mutane, da sata a faɗin jihar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Yusuf Mohammed Lawal ne, ya bayyana hakan yayin taron ƙara wa juna sani da aka yi a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri.

Hakazalika, ya bayyana nasarorin da suka samu a shekarar da ta gabata da kuma shirin da suka sa a gaba a sabuwar shekarar 2025.

A cewarsa, rundunar ta kuma gano bama-bamai 18 da ba su fashe ba, sannan sun ƙwato motocin sata 13, da bindigogi shida.

Kwamishinan, ya jaddada cewa za su ci gaba da tabbatar da tsaron mazauna jihar tare da bin dabarun da Sufeto-Janar na ’yan sanda ya shimfiɗa.

Ya bayyana cewa za su yi haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, wajen jawo hankalin jama’a su bayar da rahoton masu aikata laifuka.

A cewarsa hakan zai inganta aikin jami’an ’yan sanda, da tattara bayanan sirri a kan lokaci.

Kwamishinan, ya kuma yaba wa gwamnatin Jihar Borno, kan goyon bayanta, musamman wajen kafa dokar hana cin zarafin mutane (VAPP) da kuma dokar shari’ar laifuka (ACJA).

Ya kum buƙaci al’ummar Jihar da su ci gaba da taimaka wa rundunar wajen bayar da rahoton duk wani abu da ke da alaƙa da tsaro domin kauce wa matsaloli.