’Yan sanda sun kama mutum biyu da bindigogi 20 a Bauchi

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi Mohammed Ladan ya ce ’yan sanda masu sintiri a hanyar Bauchi zuwa Gombe sun kama wasu mutum biyu masu suna Mustapha Gona da Ali Mohammed Chibok cikin wata mota fijo dauke da bindigogi 20 da suka boye a cikin murafen kofar motar tare da harsasai 293 da makunshin harsasai 20.  […]

’Yan sanda sun kama mutum biyu da bindigogi 20 a Bauchi

Wani dan sanda yana nuna bindigogin da suka kama daga wasu mutum biyu a Bauchi.Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi Mohammed Ladan ya ce ’yan sanda masu sintiri a hanyar Bauchi zuwa Gombe sun kama wasu mutum biyu masu suna Mustapha Gona da Ali Mohammed Chibok cikin wata mota fijo dauke da bindigogi 20 da suka boye a cikin murafen kofar motar tare da harsasai 293 da makunshin harsasai 20. 

Kwamshinan ya bayyana haka ne ga manema labarai a Bauchi inda ya ce sannan a wani samame da suka kai tare da ’yan banga sun kama wani mai suna Anas dahiru a unguwar Fadamar Mada a garin Bauchi da wayoyin dalbaton na gidan talabijin na kasa da ke Bauchi na kusan Naira miliyan bakwai da ake zargin ya yanke daga tashar da ke kan Dutsen Warinje. Kwamishina Ladan ya ce suna ci gaba da bincike kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu. Ya roki jama’a su rika ba su bayanai a duk lokacin da suka ga masu aikata laifi.
A wani labarin kuma jami’an Hisbah da ke karkashin Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi sun kai samame gidajen da ake zargi na tara matan banza da otel-otel inda suka kama mata 14 da maza bakwai. Cikin wadanda aka kama an samu mata bakwai masu dauke da cutar kanjamau, inda uku suka bayyana cewa dama suna shan magani don haka ba sai an gwada su ba.
Kwamandan Hisba na Jihar Bauchi Alhaji Jibrin danlami Hassan ya ce sun fita samamen ne don rage irin abin da ke faruwa na badala a wurare daban-daban a garin Bauchi, inda suka kai samame a billa Garden da Sogiji Otel da Bauchi Club, kuma sun gurfanar da wasu daga cikin wadanda suka a kotun Unguwar Jaki ta Biyu.
Jami’in Hisbah dayyabu Ayuba ne ya gurfanar da Hindatu Shu’aibu da Aliyu Auwal Aliyu da aka kama su a Bauchi Club bisa zargin suna lalata, kuma sun amsa laifinsu inda suka nemi kotu ta musu sassauci yayin yanke hukunci, an tura su gidan yari na mako daya kafin a yanke musu hukunci.
Saura su ne Rabi Mahnmud da A’ishatu Mohammed da aka kama a Salama Guest sai Murjanatu Yusuf Gwabba da Hauwa Muhammad da aka kama a otel din Sogoji, yayin da A’ishatu Sulaiman da Halima Muhammad aka kama su a billa Garden.
Alkalin kotun Malam Hashimu Dass ya tura su zaman jiran shari’a na mako daya kafin yanke musu hukunci a karkashin dokar shari’a ta 372 da 95 ta shekarar 2001.
Alhaji Jibrin Hassan ya ce sauran mutanen ana bincike a kansu kafin a tura su kotu, saboda akwai wadanda an sha kama su har jari gwamnati ta ba su don su nemi sana’a su daina karuwanci amma aka sake kama su a wannan samame.