’Yan sanda sun kama riƙaƙƙun ’yan daba 22 a Kano

Fadan daba dai na ci gaba da yin ƙamari a unguwar Dorayi.

’Yan sanda sun kama riƙaƙƙun ’yan daba 22 a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta cafke wasu riƙaƙƙun ’yan daba 22 da suka addabi unguwar Dorayi da ke Karamar Hukumar Gwale a jihar.

Rundunar ta cafke ’yan daban ne biyo bayan fada da ya barke tsakanin wasu kungiyoyin daba guda biyu a ranar Laraba.

Wannan na zuwa ne bayan da wani faifan bidiyo ya karade shafukan sada zumunta, inda aka hangi ’yan daban na saran mutane da makamai.

Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ya bayyana sunan wasu ’yan daba 30 da ake zargi da addabar unguwar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel, ya ce zai bude sabon ofishin yaki da ayyukan daba a unguwar Dorayi.

A baya dai rundunar ta bude kofar karbar tuba da gyara daga ’yan daba a Kano, wanda hakan ya kai ga ajiye makaman kusan ’yan daba 50 a jihar.

A gefe guda kuma, rundunar ’yan sandan jihar ta shirya wasan kwallon kafa da tubabbun ’yan daba a wani sabon shiri na kyautata alaka a tsakaninsu.