’Yan sanda sun kama sama da mutum 100 saboda auren jinsi daya a Delta

An kama mutanen ne a wani itel

’Yan sanda sun kama sama da mutum 100 saboda auren jinsi daya a Delta

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta ta ce ta kama sama da mutum 100 saboda daura auren jinsi daya a wani otel da ke Jihar.

A wani sako da rundunar ta wallafa a dandalin X ranar Talata, rundunar ta ce nan ba da jimawa ba za ta yi bajekolin mutanen.

“Rundunar ’yan sandan jihar Delta ta kama sama da mutum 100 a wani otel suna bikin namiji da namiji. Nan ba da jimawa ba za mu yi bajekolinsu ta bidiyo a dandalin Facebook,” kamar yadda suka wallafa.

Tun dai lokacin da aka sanya hannu a dokar haramta auren jinsi daya a Najeriya a 2014, wadanda aka tabbatar masu auren jinsi daya ne ake kama su a damka wa jami’an tsaro.

Ko a watan Disamban 2020, sai da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ita ma ta kama mutum 10 a wani otel da ke unguwar Okota saboda auren na jinsi daya.

Dokar haramta auren jinsi daya dai ta shekara ta 2014 ta Najeriya ta yi tanadin daurin shekara 14 a gidan kaso ga dukkan wanda aka samu da aikata laifin.