’Yan sanda sun kama sarakuna 13 a Kamaru
Mukaddashin Gwamnan Lardin Arewa-mai-Nisa a garin Mokolo na kasar Kamaru, ya umarci jami’an tsaro na Jandarma da su gudanar da bincike akan wasu sarakunan gargajiya 13 masu daraja ta uku, bisa ga tuhumarsu da ake yi da dangantaka da kungiyar Boko Haram. Wannan kamen da ya gudana a jere a cikin wasu ’yan kwanaki biyu […]
Mukaddashin Gwamnan Lardin Arewa-mai-Nisa a garin Mokolo na kasar Kamaru, ya umarci jami’an tsaro na Jandarma da su gudanar da bincike akan wasu sarakunan gargajiya 13 masu daraja ta uku, bisa ga tuhumarsu da ake yi da dangantaka da kungiyar Boko Haram.
Wannan kamen da ya gudana a jere a cikin wasu ’yan kwanaki biyu bayan wasu bayanai da suka fallasa a washe garin kai hari da kungiyar Boko Haram ta yi a garin Ashigashiya wanda ya hallaka sojoji uku. Kodayake, har zuwa yanzu babu wani sakamakon da ya bayyana daga binciken da ake ma wadannan sarakunan, sai dai kuma tarin wasu masu fada a ji ne na lardin Arewa-mai-Nisa suke tsare a hannu hukuma tun lokacin da kungiyar Boko Haram ta fara mamayar lardin.
A ranar 26 ga watan Satumban bara aka tsare magajin garin Fotokol Mahamat Moussa da wasu mutane takwas bisa ga tuhumar da ake yi musu na kulla hulda da kungiyar Boko Haram. Har ila yau, a ranar 28 ga watan Nuwamba wasu mutum biyu wato dan majalisar dokoki Abba Malla da wani mutum Abdoulay su ne suka shiga hannu hukuma a dalilin cewa dan majalisar ne ya shiga tsakani wurin sasantawa da Boko Haram domin sakin wasu mutane da aka yi garkuwa da su cikinsu har da uwargidan Minista Amadou Ali. Kamar yadda hukumomi suka bayyana binciken farko ya nuna cewa mutanen biyu suna taimaka wa Boko Haram canza lambobin motocin da suke kwatowa daga Najeriya, inda suke shigo da su kasar Kamaru. Wasu na ganin cewa nasarorin da ’yan kungiyar Boko Haram suke samu a Kamaru ya biyo bayan samun goyon bayan da wasu jama’a kasar suke ba su.