‘Yan sanda sun kama sojan bogi a Delta

Babban Jami’in Hedkwatar Hukumar ‘yan sandan Ekpan SP Ibok Asamanyi a karamar hukumar Uvwie ta jihar Delta, ya ce jami’an ‘yan sandan sun kama sojan bogi mai mukamin Manjo. Wanda ake zargin sojan bogi ne mai suna Blessing Emelor ‘M’ mazaunin Isoko an kama shi ne tun a ranar 6 ga Afrilu 2019 a garin […]

‘Yan sanda sun kama sojan bogi a Delta

Babban Jami’in Hedkwatar Hukumar ‘yan sandan Ekpan SP Ibok Asamanyi a karamar hukumar Uvwie ta jihar Delta, ya ce jami’an ‘yan sandan sun kama sojan bogi mai mukamin Manjo.

Wanda ake zargin sojan bogi ne mai suna Blessing Emelor ‘M’ mazaunin Isoko an kama shi ne tun a ranar 6 ga Afrilu 2019 a garin Warri.

‘Yan sandan sun yi nasarar kama sojan bogin ne lokacin da ya baiwa wani soja mai karamin mukami umarnin budewa wasu matafiya wuta.

Kakakin hukumar ‘yan sandan ASP Chuks Orisewezie, ya ce wannan sojan bogin ya kai shekara uku yana amfani da kayan sarki na soja da sauran abin da sojoji ke sakawa a matsayin soja na asali.