’Yan sanda sun kama sojan gona a Kaduna
Sojan gonan ya shiga hannu ne bayan da wani mutum ya shigar da kara a ofishin ‘yan sanda.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama wani sojan gona da ake zargi da hannu wajen yin fashi da makami a jihar.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ne, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Kaduna.
- Matsalar Tsaro: Jami’an tsaro sun gayyaci Sheikh Gumi — Gwamnati
- HOTUNA: Yadda Peter Obi ya yi buda baki da Musulmai a Kano
Hassan, ya bayyana cewa, ’yan sanda sun kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar, biyo bayan shigar da kara da wani mutum ya yi.
Mutumin ya bayyana yadda wanda ake zargin da abokansa suka taba tare shi tare da yi masa fashi.
Wanda ya shigar da karar ya shaida wa ’yan sanda yadda wanda ake zargin tare da wasu abokansa uku suka yi masa fashin Naira 25,500 tare da kwace masa wayoyinsa a ranar 16 ga watan Maris, ta hanyar amfani da wata na’urar jan mutane.
Na’urar dai ana amfani da ita ne don rage kuzarin mutane. Kuma na’urar tana kama da bindiga.
Hassan, ya bayyana cewa, binciken da aka yi a gidan wanda ake zargin ya kai ga gano wasu kayan laifi, ciki har da kakim soja da wasu makamai.
Ya tabbatar da cewa za su gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.