’Yan Sanda Sun Kama Sojoji 4 Kan Fashi Da Makami

Sojojin sun bar wurinsu sun je wata jihar yin harkallar da suka fada a hannun ’yan sanda

’Yan Sanda Sun Kama Sojoji 4 Kan Fashi Da Makami

Wasu sojoji guda hudu da wani babban jami’in hukumar Sibil Defens sun shiga hannun ’yan sanda bisa zargin fashi da makami.

Rundunar ’yan sandan jihar Ribas ta kama jami’an tsaron guda biyar da wasu fararen hula guda tara, bisa zargin su da fashi da makami da kuma karkatar da wasu manyan motoci.

A ranar Litinin ne kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar.

Ta ce an kamo wadanda ake zargin ne bayan wani bincike da aka yi ta hanyar damke wasu da suka fasa wani katafaren rumbu da ke unguwar Elimgbu, karamar hukumar Ohio/Akpor.

Ta bayyana cewa an gano cewa biyu daga cikin wadanda ake zargin sojoji ne masu mukamin kofur ne da ke aiki a jihar Delta da kuma jami’in hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya da ke aiki a Kabba, jihar Kogi.

Ta ce jami’an tsaron da aka kama sun amsa cewa sun gudu daga wurin da aka ajiye su su yi aiki ne suka tafi aikata laifukan a jihar Ribas.

Iringe-Koko ta ce, bincikensu ya gano wani gungun masu aikata laifuka da ke da hannu a fashi da makami, satar mutane da kuma karkatar da motoci.

Ta kara da cewa barayin na da hannu wurin yin awon gaba da tireloli da ke dauke da kayayyaki daban-daban da suka hada da takin zamani, tufafin da ake shigowa da su kasar waje, da kuma simintin POP.

Sanarwar ta ce, an kori sojojin da ake zargi bayan tabbatar da laifinsu an kuma mika su ga ’yan sanda domin ci gaba da bincike da gurfanar da su ga kotu.