’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano
Rikicin da ya janyo asarar rayuka da raunata wasu, kuma ya yi sanadin asarar kadarorin jama’a da dama a yankin.
Jami’an ‘yan sanda da aka tura Unguwar Kofar Mata/Zango da ke kusa da Asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano sun kama wani matashin mai suna Kabiru Jamilu mai shekara 21, mazaunin rukunin gidaje na Zango Quarters Kano.
Kabiru wanda aka bayyana shi a matsayin wanda ya kitsa rikicin ‘yan daba da ya ɓarke tsakanin ’yan daba na Kofar Mata da matasan Zango da ya faru kwanan nan.
- Ɗan Gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa
- Mutum 38 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama a Kazakhstan
Rikicin da ya janyo asarar rayuka da raunata wasu, kuma ya yi sanadin asarar kadarorin jama’a da dama a yankin.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin jagorantar faɗan da aka yi.
Kiyawa ya ci gaba da cewa, binciken ne ya kai ga kama Umar Garba mai shekara 32, mazaunin Zango Ƙuarters Kano, wanda aka same shi da wata doguwar wuƙa mai kaifi.
Kiyawa ya ƙara da cewa, an miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar (CID) kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.