’Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da kisan dan kasuwa a Bayelsa

’Yan sandan Bayelsa sun tabbatar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen kashe wani dan kasuwa, mai suna Mista Akunama Agunza. Kuma wadanda ake zargi da aikata laifi, ana ganin  jami’an tsaro ne.Wakilinmu ya gano cewa, an halaka mutumin ne a lokacin da yake kokarin fansar kwale-kwalensa da rundunar tsaron hana […]

’Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da kisan dan kasuwa a Bayelsa
’Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da kisan dan kasuwa a Bayelsa

’Yan sandan Bayelsa sun tabbatar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen kashe wani dan kasuwa, mai suna Mista Akunama Agunza. Kuma wadanda ake zargi da aikata laifi, ana ganin  jami’an tsaro ne.
Wakilinmu ya gano cewa, an halaka mutumin ne a lokacin da yake kokarin fansar kwale-kwalensa da rundunar tsaron hana satar mai ta kama, a karamar Hukumar Kudancin Ijaw.
An bayyana cewa mamacin ya bayar da hayar kwale-kwalensa ne ga wawsu matasa, wadanda suka yi amfani da shi wajen satar man, har aka kama su. Kuma kokarin da mai kwale-kwalen ya yi na karbo abinsa ,aka kashe a wani irin yanayi mai wuyar sha’ani.
Shi kuwa mai magana da yawun iyalan mamacin, Silas Okiri, cewa, ya yi, an kai rahoton abin ya auku a ofishin ’yan sanda ke Oporoma, bayan da suka gano rubabbiyar gawar Akunma Agunza a kogin Ofonigbene da ke Kudancin Ijaw.
Okiri ya ce duk da cewa wadanda ake zargi suna rike wayoyin hannun mamaci, dakwale-kwalensa,sun kasa yin bayaninindan zdan uwansu ya shige.
Shi kuwa mai magana da yawun ’yan sanda, Mista Aled Akhigbe, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ana ci gaba dagudanar dabincike.