’Yan sanda sun kama wadanda suka daure ’ya’yansu 13 da sarka a Amurka
Wadansu ma’aurata da ke zaune a Kudancin California sun shiga hannun ’yan sanda bayan da aka gano yadda suka daure ’ya’yansu 13 a jikin gadaje da sarka, kuma an bar su babu isasshen abinci. Dabid Allen Turpin mai shekaru 56 da matarsa Louise Ann Turpin mai shekara 49, wadanda dukkansu ke zaune a Prrris, wani […]
Wadansu ma’aurata da ke zaune a Kudancin California sun shiga hannun ’yan sanda bayan da aka gano yadda suka daure ’ya’yansu 13 a jikin gadaje da sarka, kuma an bar su babu isasshen abinci.
Dabid Allen Turpin mai shekaru 56 da matarsa Louise Ann Turpin mai shekara 49, wadanda dukkansu ke zaune a Prrris, wani gari mai nisan kilomita 100 daga gabashin Los Angeles, an kama su ranar Lahadin da ta gabata kan zargin azabtarwa da keta haddin kananan yara, kamar yadda aka bayar da sanarwa daga ofishin ’yan sanda na Riberside County Sheriff.
’Yan sandan yankin da mataimakansu daga ’yan sandan Sheriff sun isa unguwar ne inda wani daga cikin yaran mai shekara sha wani abu ya tsere, kuma sun yi matukar kaduwa da suka ga halin da yaran ke ciki.
“Binciken da aka ci gaba da gudanarwa ya bayyana cewa akwai dimbin yaran da aka daure su da sarka a jikin gado aka garkame da kwado, kuma suna zaune a cikin duhu a wuri mai wari,” kamar yadda sanarwar jami’an ta nuna.
“Jami’an sun gano sauran yara 12 da ke tsare a cikin gida, amma sun yi matukar kaduwa ganin cewa bakwai daga cikinsu duk manya ne, wadanda shekarunsu ya kama daga 18 zuwa 29.”
Yaran dai sun jikkata alamu sun nuna “ba su samun isassshen abinci” kuma “suna cikin dauda,” a cewar sanarwar, inda aka kara bayyana cewa tuni aka kai su asibiti bayan da ’yan sandan suka tattauna da su.
Daga nan sai aka tsare Dabid da Louise Turpin, inda za a ci gaba da azabtar da su, tare da sharadin beli na Dala miliyan tara ga kowanensu.