’Yan sanda sun kama wadanda suka kashe mata biyu saboda zargin maita

Yan sandan jahar Jigawa sun kama mutane biyu wadanda suka kashe wadansu tsofaffin mata biyu suka kuma cinna wa gidan da suke zaune wuta saboda suna zarginsu da maita.Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘Yan sandan jihar Jigawa, Abdul Jinjiri ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ‘yan sandan ta yi sa’ar cafke mutum biyun da […]

’Yan sanda sun kama wadanda suka kashe mata biyu saboda zargin maita
’Yan sanda sun kama wadanda suka kashe mata biyu saboda zargin maita

Yan sandan jahar Jigawa sun kama mutane biyu wadanda suka kashe wadansu tsofaffin mata biyu suka kuma cinna wa gidan da suke zaune wuta saboda suna zarginsu da maita.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘Yan sandan jihar Jigawa, Abdul Jinjiri ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ‘yan sandan ta yi sa’ar cafke mutum biyun da suka yanka wadannan tsofaffin matan. Ya ce rundunar ta cafke “Sani Malam Yelwa dan shekara 30, da Rilwanu Suleiman mai shekara 52, bisa zargin kashe Asiya Malam Sule ‘yar shekara 65 da Lami Alhaji dahiru 56 saboda zargin cewa mayu ne.”
Sani da Rilwanu ‘yan uwan Abubakar Suleman ne wanda ake zargin ya mutu saboda wadannan mata da ake zargin mayu ne suka kashe shi ta hanyar maita.    
 A makon da ya wuce ne a kauyen Kira da ke yankin karamar hukumar Gwaram ta jahar Jigawa
aka yanyanka Asiya Malam Sule ‘yar shekara 65 da ‘yarta Lami Alhaji dahiru, aka kuma kona gidansu.
Kakakin ‘yan sandan ya ce kisan wannan mata tare da ‘yarta ya biyo bayan mutuwar wani saurayi ne mai suna Abubakar Sulaiman, mai shekaru 20 da haihuwa, wanda makwabcin gidan da wadannan matan suke zaune ne wanda mutane suke zargin sune suka kashe wannan saurayin.
 Da Aminiya ta tattauna da daya daga cikin ‘ya’yan marigayiyar wanda dalibi ne a kwalejin ilimi taSa’adatu Rimi da ke Kano, mai suna Sani dahiru, ya ce mutanen unguwar sun afka wa gidansu ne suka kashe mahaifiyarsa da kanwata a sakamakon mutuwar wani yaro makwabcinmu.’’
Ya ci gaba da cewa, ‘’kimanin shekaru uku da suka gabata dan uwan Abubakar sule ya kwanta rashin lafiya har ya rasu, wanda daga bisani suka ce wai mu mayu ne kuma mune muka kashe shi, hakan ta sanya sai da aka je kotun shari’ar musulunci kafin a warware wannan matsalar, kuma wallahi mu ba mayu ba ne, ba mu ma san mene ne maitar ba ballantana mu cinye wani mutum, wallahi.”
Sani ya kara da cewa, ‘’daga bisani wannan dan uwa nasa shi ma ya kwanta rashin lafiya kuma har ya rasu, shi ne suka afka wa gidan namu, amma kafin karasowarsu gidan mutanen mutanen gidan muka gudu, sai mahaifiyata wadda tsohuwa ce tare da kanwata inda suka yi musu kisan-gilla ta hanyar yanka su gunduwa-gunduwa. Na rantse da girman Alkur’ani ba mu san mece ce maita ba kuma mu ba mayu ba ne, amma saboda rashin gata ganin cewa mu ba masu kudI ba ne suka tsane mu tare da aikata wannan aikin rashin imani a kanmu. Kuma har yanzu da nake magana da ku din nan sun tarwatsa mutanen gidanmu ba mu ma san inda za mu same su ba, kuma ni dai ba zan dauki wani lauya ba sai dai ina kira ga gwamnati da ta bi mana hakkinmu tare da yi mana iyaka da wadannan marasa imani da sukatsane mu.’’
Bayanai sun tabbatar cewa ‘yan sanda za su gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu kwanan nan.