’Yan sanda sun kama wanda ake zargi da harbe dan Majalisar Wakilai
’Yan Sanda sun kama mutum daya da ake zargi da bindige dan Majalisar Wakilai, Temitope Olatoye Sugar a Jihar Oyo. An bindige dan majalisar ne a yammacin ranar Asabar 9 ga Maris a garin Lalupon kusa da Ibadan bayan kammala zaben Gwamna da ’yan Majalisar Dokokin Jihar. Mataimakin Sufeto Janar mai kula da Shiyya ta […]
’Yan Sanda sun kama mutum daya da ake zargi da bindige dan Majalisar Wakilai, Temitope Olatoye Sugar a Jihar Oyo. An bindige dan majalisar ne a yammacin ranar Asabar 9 ga Maris a garin Lalupon kusa da Ibadan bayan kammala zaben Gwamna da ’yan Majalisar Dokokin Jihar.
Mataimakin Sufeto Janar mai kula da Shiyya ta 11, Leye Oyebade da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Shina Olukolu sun fadi a ranar Litinin cewa kisan da aka yi wa dan majalisar ba ya da nasaba da zaben ranar Asabar.
Mataimakin Sufeto Janar Oyebade ya ce, ’yan sanda sun samu cikakkiyar shaidar da ta kai su ga kama wanda ake zargin shi ne ya harbi dan majalisar da bindiga a kokon kansa inda ya mutu a Asibitin Koyarwa na UCH da ke Ibadan, lokacin da likitoci suke aikin ceto ransa.
“Mun kama wanda ake zargin amma ba za mu yi bayanin komai a yanzu ba,” inji Leye Oyebade, wanda ya ci gaba da cewa “Ina tare da
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo a lokacin da na ziyarci Asibitin UCH a ranar Asabar don ganawa da Shugaban Asibitin.” Ya ce suna yin aiki ne kamar yadda Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya ba su umarni don zakulo dukan masu hannu a wannan al’amari domin a hukunta su.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Shina Olukolu ya yi karin haske a kan rahoton da ya fara samu daga DPO din ofishin ’yan sanda na Iyana Offa cewa an harbi dan majalisar ne a wani kwanton bauna da aka yi a daidai lokacin da yake duba yadda aka yi zaben Gwamna da ’yan majalisa a ranar.
Dangane da rikicin siyasa a rumfunan zabe a Jihar Oyo, shugabannin ’yan sandan biyu sun tabbatar da kama mutum 18 da bindigogi 6 da albarusai 9 da adduna da wukake da sauran abubuwan da aka haramta amfani da su a wannan lokaci.