’Yan sanda sun kama wanda kashe matarsa ya gudu

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta samu nasarar kama wani matashi da ake zargi da kashe matarsa da fatanya kimanin wata shida da suka gabata saboda ta ki amincewa ta koma gidansa. Rundunar ta kuma kama wadansu da ake zargin su ne suka addabi mazauna birnin Dutse da Karamar Hukumar Gwiwa wajen aikata fashi da […]

’Yan sanda sun kama wanda kashe matarsa ya gudu

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta samu nasarar kama wani matashi da ake zargi da kashe matarsa da fatanya kimanin wata shida da suka gabata saboda ta ki amincewa ta koma gidansa. Rundunar ta kuma kama wadansu da ake zargin su ne suka addabi mazauna birnin Dutse da Karamar Hukumar Gwiwa wajen aikata fashi da makami.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, matashin da ake zargi da hallaka matar tasa mai Shu’aibu Haro mai kimanin shekara 30 ya ce a lokacin da ya sa fatanya ya sare ta, sai ya sanar da abokinsa ya je ya dauke ta zuwa asibiti saboda a zatonsa  za ta rayu.

Ya ce daga nan ne ya gudu ya bar kauyensu na Warwade ya koma yana kwana a runfunan kasuwa a tsakanin garuruwan Andaza da Shuwarin. Ya  ce ya dawo ne yanzu a saboda tunanin maganar ta wuce, amma sai ’yan sanda suka kama shi.

Shi kuwa Suleiman Mukhtar mazaunin Unguwar Danmasara, ya ce  ’yan sanda  masu sintiri ne suka kama shi ne a lokacin yake kokarin sayar da da wasu manyan katifu da ya sato daga gidanjen da ya balle lokacin da masu gidajen suka ta fi bikin Kirsimeti.

Suleiman Muhtar ya ce aure yake nema zai yi, kuma rashin kudin da zai yi wa budurwar tasa hidima ce ya jefa shi cikin wannan danyen aiki.

Suleiman wanda bai wuce shekara 23 ba, cikin kuka ya bukaci rundunar ’yan sandan ta taimaka ta yi masa sassauci, kasancewar wannan shi ne karo na farko da ya aikata sata.

Shi kuwa wani matashi mai suna Ibrahim Audu mai shekara 27 mazaunin kauyen Katseyal da ke Karamar Hukumar Sandamu a Jihar Katsina ’yan sanda sun kama shi ne dauke da wasu kananan bindigogi kirar gargajiya yana jiran abokan harkarsa a wani kauye don fita zuwa sata.

Ya ce sun jima suna kai wa masu kudi mazauna yankin hari suna amsar kudade a wajensu, ya ce ko a wannan karon rana ce ta baci, saboda ya zuba bindigogin ne a cikin ledar bakko yana yawo da su, kuma dare ya yi, shi ne ’yan banga suka kama shi suka kwace ledar da kokawa suka daure shi.

Ya ce bayan sun kayar da shi ne, suka daure shi suka mika wa ’yan sanda shi. Ya ce bai ji dadin yadda aka kama shi ba, kuma ya yi nadamar shigarsa fashi da makami.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, SP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa da zarar sun gama bincike za su gurfanar da su  a gaban kotu.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta