‘Yan sanda sun kama wanda suka yi garkuwa da yara 2 a Abuja
Hukumar `yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ce, ta kubutar da yara biyu da aka yi garkuwa da su, yayin da suka kama mutum uku da ake zargin su ne suka yi garkuwa da yaran unguwar Zuba da ke Abuja. Wadanda ake zargin sun hada da: Nasiru Mohammed mai shekara 20 da Sale Bello […]
Hukumar `yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ce, ta kubutar da yara biyu da aka yi garkuwa da su, yayin da suka kama mutum uku da ake zargin su ne suka yi garkuwa da yaran unguwar Zuba da ke Abuja.
Wadanda ake zargin sun hada da: Nasiru Mohammed mai shekara 20 da Sale Bello mai shekara 19 da kuma Hassan Audu mai shekara 20.
Kwamishinan ‘yan sandan Abuja Mista Bala Ciroma ne bayyanawa manema labarai hakan a jiya Laraba a Abuja.