An Kama Dan Sandan Da Ya Harbe Mai Talla A Kasuwar Abuja
Ana zargin cewa matashin da ake tuhuma a wata kotun tafi-da-gidanka ya yi yunƙuri tserewa daga hannun ’yan sanda.
Rundunar ‘yan sandan Abuja ta ce ta kama Usman Ishaya Magaji, jami’in dan sandan da ake zargi ya harbe Ibrahim Yahaya wani matashi da ke talla a Kasuwar wuse ranar Talata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Adeh Josephine ce ta tabbatar da kamun ta wayar tarho ga wakilinmu da yammacin ranar Talata.
SP Josephine ta ce wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda a halin yanzu, kuma za a ci gaba da bincike.
- Abin Da Addini Yace Game Da Azumin Ƙananan Yara
- ’Yan bindigar da suka sace ɗaliban Tsangaya a Sakkwato sun buƙaci fansar N20m
Aminiya ta ruwaito cewa, wasu fusatattun matasa da yammacin ranar Talatar da ta gabata sun kona wasu sassa na kasuwar Wuse da ke Abuja, ciki har da wasu motoci da aka ajiye a cikin kasuwar, bayan da ‘yan sanda suka harbe matashin mai shekaru 17 da haihuwa.
An ce marigayin da ake tuhuma a kotun tafi-da-gidanka da ke cikin kasuwar ya yi yunkurin tserewa, inda nan take ‘yan sanda suka harbe shi, kuma nan take ya ce ga garinku.
Wannan lamari dai kamar yadda rahotanni suka tabbatar shi ya fusata wasu ’yan kasuwar kuma ake zargin su da nuna fushinsu ta hanyar ƙone-ƙone a sassan kasuwar.
Bayan afkuwar lamarin, kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Benneth Igweh, ya jagoranci wasu jami’an rundunar zuwa wurin da lamarin ya faru domin tantance barnar da ‘yan ta’addan suka yi.